A lokacin da nake zaune ni ɗaya na fi jin daɗin rubuta labari – Fatima Jibrin

LAFAZI WRITERS ASSOCIATION

SHIRIN MU SAN JUNANMU

Masu Gabatarwa:
(i) Surayya Dahiru
(ii) Aseeya Muhammad
(iii) Sadik Abubakar

Rana: 20 ga Agusta 2023.

Lafazi: Assalama Alaikum Warahamatullah Wabarakatuh.

Barkan mu da wannan lokaci, da fatan mun yini lafiya, ya kujiba-kujibar yau da kullum? Allah Ya yi mana jagora.

In Sha Allah yanzu za mu fara gabatar da shirin MU SAN JUNANMU, kamar yadda aka sani shiri ne da zai riƙa zaluƙo mambobin wannan ƙungiya ta Lafazi Writers Association ana yin hira da su, domin ƙarfafa zumunci da ƙara ƙulla danganta kyakkyawa.

A cikin shirin namu na wannan mako, wanda ya kasance na farko, mun karɓi baƙuncin ɗaya daga cikin daɗaɗɗun mambobin wannan ƙungiya, watau Fatima Jibrin.

A madadina da sauran masu gabatar da shirin, muna yi wa babbar baƙuwarmu barka da zuwa.

Fatima: Wa’alaikumus salam barka dai.

Lafazi: MALAMA FATIMA KAFIN MU TSUNDUMA CIKIN SHIRIN ZA MU SO MU JI ƊAN TAƘAITACCEN TARIHINKI

Fatima: Kamar yadda kuka sani sunana Fatima Jibrin, an haife ni a garin Zariya, kuma na yi makaranta tun daga ajin yara har sakandire a garin Zariya kafin na samu admission (gurbin karatu) a Kwalejin Ilimi ta Tarayya, watau Federal College of Education Zaria, a inda nake karantar Biology Inter Science. Wannan shi ne taƙaitaccen tarihina.

Lafazi: SHIN ME YA JA HANKALINKI KIKA SHIGA DUNIYAR RUBUTU?

Fatima: Ni dai tun ina ƙarama ina son karatun novels, na fara ne daga karanta Magana Jari Ce da Gishirin Zaman Duniya. Nakan ƙirƙiri labari na rubuta shi a takarda. A haka dai har na fara sauraren shirin Gobe Da Labari wanda ake yi a Alheri Radio, kullum dai burina na ga ni ma na rubuta nawa littafin.

Gaskiya babban abin da ya sa na shiga duniyar rubutu shi ne; na fahimci ta hanyar rubutu za ka iya isar da saƙonka, ma’ana za ka faɗakar, ilmantar da sauransu.

Lafazi: WACE SHEKARA KIKA FARA RUBUTU, KUMA LITTAFAI NAWA KIKA RUBUTA?

Fatima: Na fara rubutu a shekarar 2021, na fara rubuta littafai guda biyu, amma nakan rasa su idan wayata ta samu matsala. Don haka har yanzu dai Allah bai nufa na kammala ko guda ɗaya, amma in sha Allah zan kammala rubuta littafina na farko nan ba da jimawa ba.

Lafazi: WASU MARUBUTAN KAN SAMU JIGO YAYIN DA SUKE BARCI A CIKIN MAFARKINSU, WASU KUMA LOKACIN AIWATAR DA WANI AIKI. SHIN KE TA YA YA KIKE SAMUN JIGO?

Fatima: A lokacin da nake yin aiki.

Lafazi: MALAMA FATIMA, TSAKANIN SUNAN LABARI DA KUMA JIGO WANNE KIKE FARA SAMU, SANNAN WANNE YA FI MIKI SAUƘIN SAMU?

Fatima: Gaskiya jigo ya fi mini saukin samu kuma shi nake fara samu saboda wani lokacin sunan labari na ba ni wahalar samu.

Lafazi: A WANE IRIN LOKACI KIKA FI JIN DAƊIN RUBUTA LABARI, SANNAN A WANE YANAYI? IDAN NA CE YANAYI, INA NUFIN YANAYIN WALWALARKI, WASU MARUBUTAN IDAN SUNA CIKIN FARINCIKI SUN FI YIN RUBUTU. KE YA YA ABIN YAKE A WAJENKI?

Fatima: A lokacin da nake zaune ni ɗaya na fi jin daɗin rubuta labari, kuma ya kasance idan ina farinciki.

Lafazi: WASU MARUBUTAN KAN KOKA CEWA IDAN SUKA FARA RUBUTA LABARI, SAI SU KAKARE, SHIN KIN TAƁA FUSKANTAR HAKAN?

Fatima: E, na taɓa ba sau ɗaya ba ma.

Lafazi: A WANE LITTAFI NE KIKA FUSKANCI HAKA KUMA YA AKA YI KIKA WARWARE MATSALAR?

Fatima: A littafin SANADIN MAHAIFIYATA ne, na warware matsalar ce ta hanyar karanta wani littafi wanda yanzu na manta sunansa gaskiya.

Lafazi: YA YA ZA KI KWATANTA NAGARTAR RUBUTUN YANAR GIZO (ONLINE) DA NA ƊAB’I, WATAU WANDA AKE BUGAWA A TAKARDA?

Fatima: Kowanne da nagartarsa, ban san wanda ya fi wani nagarta ba.

Lafazi: AN CE MARUBUTAN ONLINE KUN FI SAMUN KUƊI, WAI KUNA IYA SAMUN MAƘUDAN KUƊAƊE A LITTAFI ƊAYA KACAL. SHIN KE MA KINA SAMUN HAKAN KO MAKAMANCIN HAKAN?

Fatima: Gaskiya tunda ban wallafa ba ban fara samun kuɗin ba, sai nan gaba zan tabbatar da haka.

Lafazi: ANA ZARGIN MARUBUTAN ONLINE DA YAƊA BATSA A CIKIN AL’UMMA, WANDA HAKAN NA BA DA GUDUMMAWA WAJEN LALATA TARBIYYA. WANE KIRA ZA KI AKAN WANNAN BATU?

Fatima: Gaskiya masu yin haka su ji tsoron Allah su tuna duk abin da ka rubuta za a yi hisabi a kansa, marubuta kamata ya yi su yi ƙoƙarin gyara tarbiyya ba lalatawa ba. Kuma suna ɓata mana suna Allah ya shirya.

Lafazi: SHIN ME KIKA ƊAUKI RUBUTU, DON NISHAƊI KO KUMA SANA’A?

Fatima: E to, zan iya cewa duka biyun domin ina jin nishaɗi idan ina rubutu.

Lafazi: AKAN SA WA MARUBUTA GASA TA RUBUTA LABARI, INA JIN YAU ƊIN NAN MA AKE SHIRIN RUFE KARƁAR LABARAI A GASAR MARUBUTA MATA TA BBC HAUSA MAI TAKEN HIKAYATA. SHIN KINA SHIGA IRIN WAƊANNAN GASANNI?

Fatima: E, na shiga sau ɗaya. Gasar Hikayata BBC Hausa a shekarar 2022.

Lafazi: A KOWANE ABU DA ƊAN’ADAM YAKE YI BA A RASA KALUBALE TATTARE DA WANNAN ABU, SHIN WANE ƘALUBALE KIKA FUSKANTA A HARKAR RUBUTU?

Fatima: Ƙalubalen da na fuskanta shi ne, duk lokacin da na fara rubuta labari sai na rasa wayar, ko ya lalace hakan na sa na rasa labarin da na rubuta. Wannan kaɗai ne ƙalibalena.

Lafazi: IDAN HAR AN YI MAGANAR ƘALUBALE TILAS KUMA A AMBACI NASARORI, WAƊANNE NASARORI KIKA SAMU A HARKAR RUBUTU?

Fatima: Na samu damar cuɗanya da marubutan da na karanta littafansu wanda ban taɓa tunanin zan samu wannan damar ba. Sannan na samu magoya baya waɗanda ko yau na wallafa littafi za su karanta Alhamdulillah!

Lafazi: BAYAN RUBUTUN LITTAFI, SHIN KINA WATA SANA’AR NE?

Fatima: E to, za a iya kira na cima zaune, domin ba na wata sana’ar amma ina tunanin farawa. Ina da burin zama babbar marubuci ya wacce za a karanta littafinta a ko’ina.

Lafazi: WANE ABU NE IDAN KIKA TUNA SHI A RAYUWARKI YAKE SA KI FARINCIKI HAR KI YI DARIYA KO DA KUWA KE KAƊAI CE A WAJE?

Fatima: Idan na tuna yadda iyayena ke ba ni goyon baya a dukkan abin da na sa gaba, indai bai kauce hanya ba. Sannan idan na tuna yadda Allah Ya cika mini buruka.

Lafazi: WANE IRIN ABINCI DA ABIN SHA KIKA FI SO?

Fatima: Na fi son Indomie mai yaji da zafinta ko Alkubus, sai kuma kunun aya.

Lafazi: SHIN MALAMA FATIMA TA SHIGA DAGA CIKI (MA’ANA AURE) KO DAI TANA SHIRIN SHIGA?

Fatima: A’a ban riga na shiga ɗin ba tukunna.

Lafazi: WANE KIRA ZA KI YI GA MATASAN MARUBUTA IRIN KI DANGANE DA RUBUTU?

Fatima: A dage da rubutu kar a bari son jiki ya hana.

Lafazi: MENE NE SAƘONKI NA ƘARSHE?

Fatima: Ina yi wa kowa fatan alkhairi, Allah Ya ba mu sa’a a dukkan abin da muka sa a gaba na alkhairi. Allah Ya bar zumunci.

Lafazi: Allahumma amin summa amin. Malama Fatima Jibrin muna matukar godiya da amsa wannan gayyatar.

A madadina da sauran masu gabatar da wannan shirin watau Surayya Dahiru da Aseeya Muhammad⁩ sai kuma hukumar gudanarwar kungiyar Lafazi Writers Association, muna yi miki fatan alkhairi Allah Ya huce gajiya.

ALAMOMIN RUBUTUN HAUSA

©taskarlafazi



1. AYA ( . )

Wata alama ce da ake amfani da ita domin tsayawa a magana ko a rubutu. Ana amfani da aya ya yin da aka zo ƙarshen magana ko ƙarshen jawabi ko kuma wajen hutawa a ƙarshen zance.

A rubutun Hausa aya ta kasu kashi uku kamar haka:
• babbar aya ( . )
• ayar tambaya ( ? )
• alamar motsin rai ( ! )


Babbar Aya ( . )

Babbar aya na nufin babbar alamar dakatawa tare da cikakken hutu ga mai karatu da rubutu.
Irin wannan dakatawa ana amfani da ita bayan jimla ta kammala sosai, kuma ta ba da ma’ana mai gamsarwa.

Abin nufi a nan alama ce da ake amfani da ita inda ake so a tsaya
ko don a huta ko don a canja magana. Haka zalika ana amfani da ita a wasu wuraren daban.
Misali
*_Dirowata da daga jirgi ke da wuya na sauke dara-daran idanuna kan kyakkyawar fuskar Fatima. Wani siririn murmushi ta watso mini sannan cikin zazzakar muryarta ta ce, “Sannu da sauka mijina! Na yi kewar ka sosai.”_*


Ayar Tambaya ( ? )

Ayar tambaya na da ƙa’idoji iri ɗaya da babbar aya. Sai dai abin da ya bambanta su shi ne, ayar tambaya ana amfani da ita ne jimlar da ke nuna tambaya, sai a sanya ta a ƙarshen jimla, wato a muhallin da ake sanya babbar aya. Kuma ana amfani da alamar tambaya ko da a gaɓa ɗaya ce, matuƙar ta nuna tambaya.
Misali:
– Wa?
– Me?
– Ina mutane Lafazi suke?
– Ya ya sunanki?


Alamar Motsin Rai ( ! )

Kamar ayar tambaya, ita ma alamar mostin rai ko ayar mostin rai na da ƙa’idoji irin na babbar aya. Sai dai ita wan

2. WAƘAFI ( , )

Waƙafi na nufin alamar dakatawa ta ɗan lokaci. Idan mai karatu ya ci karo da wannan alama ta waƙafi (,) zai ɗan tsaya ba da jinkiri da yawa ba, domin mai karatu ya sami damar yin numfashi kaɗan, sai kuma ya ci gaba da karatu. Bayan an yi amfani da waƙafi da ƙaramin baƙi ake tashi, sai dai wajen da za a tashi da suna na zahiri. Kuma yana zuwa ne a tsakiyar ko cikin jimla, ma’ana ba a amfani da shi a ƙarshen jimla.

Ana amfani da waƙafi a wurare da dama a daidaitacciyar Hausa. Wasu daga cikin wuraren da ake amfani da shi sun haɗa da:


3. RUWA BIYU ( : )

Ruwa biyu alama ce ta dakatawa kamar aya. Ana amfani da ruwa biyu ( : ) a wurare da dama wanda suka haɗa da:

1. Yayin da za a rubuta maganar wani. Misali: Malam ya ce: “Kowa ya zauna.”

2. Yayin da ake lissafa abubuwa. Misali: kowa ya kawo waɗannan: biro; da littafi; da jaka.

2. Yayin da mutum ya zo rubuta lokacin. Misali: ana zuwa makaranta ƙarfe 2:00


4. WAƘAFI MAI RUWA ( ; )

Waƙafi mai ruwa na da hukunce-hukunce waƙafi a wani ɓangaren, sai dai ya fi kusa da aya, domin maganar da za ta biyo bayansa tana iya zama farkon magana, kusan mai cin gashin kanta.

5. ZARCE ( … )

Alama ce da ake amfani da ita a rubutu don nuna wa mai karatu cewa maganar da ake cikin yi ba ta ƙare ba, watau ana nufin da sauran magana. Wannan alama na nuna cewa an tsaya ne kawai amma akwai sauran magana ko dai an bar wa mai karatu ya cika da kansa ko abin da aka bari ba a kawo ba ba shi da muhimmanci ga jawabin da ake ciki.

Saboda haka ne wasu daga cikin karuruwan maganar Hausa ake amfanai da zarce a ƙarshensu domin a ba mai karatu damar ya cikasa da kanshi.
Misali:
– yaro bai san wuta ba sai…
– a bar kaza cikin…
– ba a san maci tuwo ba…
– kowa ya ci zomo…

6. BAKA BIYU ( )

Baka biyu alama ce da ake amfani da ita domin ƙarin bayani. Ana rubuta ƙarin bayani a cikin baka biyu ne domin ƙara ba da hasken wata kalma a cikin jimla. Ana sanya ƙarin bayani a tsakiyar baka domin ba da ma’anar wata kalma musamman ta wani harshe ko wani karin harshe, sannan kuma ana amfani da baka biyu domin tabbatar da wata hujja ta
ilimi.

Ga misalan amfani da baka biyu a rubutun Hausa:
– Audu ya ci masa (waina).

– Mutanen suna cikin danja (haɗari).

– Na ba shi N2000 (naira dubu biyu).

– Ina sha’awar masa (waina)

Duk waɗannan da aka sanya a cikin baka biyu ƙarin bayani suke yi, don haka, ba dole ne a karanta su a bayya ne ba, idan ana karatu.

7. ALAMAR ZANCEN WANI (“ ”)

Alamar zancen wani, alama ce da ake amfani da ita yayin da mutum yake maimaita maganar wani kai tsaye a cikin rubutunsa. Yawancin ana gabatar da kalmar ‘ya ce’ kafin a kawo abin da wani ya ce. Alamar zancen wani tana nuni ne ga zancen wani ba mai rubutu ba.

Kowanne baƙi ko wasali da zai zo bayan alamar zancen wani ana rubuta shi babba. Saboda magana ce sabuwa za a fara, kuma bisa ƙa’idar rubutun Hausa duk sabuwar magana da babban baƙi ko babban wasali ake fara ta.

Ga misalin amfani da alamar zancen wani:
*_Surayya ta ce: “Ana amfani da alamar zancen wani lokacin da marubuci ya kawo zancen wani kai tsaye a rubutunsa.”_*

Don haka, ya kamata marubuta su kiyaye.

8. KARAN ƊORI ( – )

Karan ɗori na ɗaya daga cikin alamomin rubutun Hausa. Wata alama ce da ake amfani da ita a rubutu a tsakanin kalmomin ko harufa. Ana amfani da karan ɗori wajen gwama kalmomin masu ma’ana daban wuri ɗaya, domin idan ba a yi amfani da alamar ba ma’anar kalmomin da aka gwama ko ake son a gwama ta fuskar ma’ana ba za ta fito sosai ba.

Ana amfani da karan ɗori ne wajen haɗa kalmomin biyu ko fiye domin su zama kalma ɗaya, musamman wajen samar da harɗaɗɗen suna.
Misali:
– haɓar-kada
– gama-gari
– shaci-faɗi
– babba-da-jaka
– riga-kafi

Duk waɗannan kalmomin da aka kawo sun ƙunshi fiye da kalma ɗaya a cikinsu, amma an
yi amfani da karan ɗori domin haɗa su ta fuskar ma’ana.

HALINA NE

HALINA NE!

Mutanen da ke sanye cikin fararen kaya nake ƙarewa kallo, tare da wangamemen ɗakin da ke jere da gadaje wanda na kasance a kan ɗaya daga cikinsu, hakan ya kunna na’urar tunanina wacce ta tabbatar mini cewa asibiti ne. To me ya kawo ni nan kuma? Na faɗa a raina tare da yunƙurin tashi zaune, raɗaɗin zafin da ya ratsa sassan jikina ne ya sa ni sakin ƙara, matan da ke tsaye kaina suka ce, koma ki kwanta tukunna. Gajeren nishi na ja, masarrafar tunanina ta shiga hakaito mini rayuwar aurena zango-zango.


Safiyar ranar da muke cika wata guda da aure ni da mijina Isma’il, na gabatar masa da batun ankon ƙawata Zainab. Cikin sakin fuska da lallausan murmushi ya ce, “Ba ki da dama, ke da ba ki jima ba wace fita za ki yi?”

“Ban gane ban jima ba? Me kake nufi ne?” A gadarance na faɗi maganar ina nuna rashin amincewa da shingen da yake shirin gindaya mini.

A fara’ance ya ce, “Ina nufin bai kamata ki fara fita ba, dududu yaushe aka kawo ki?

Tamkar ya watso mini wuta a zuciya haka na ji, nan fa hayayyaƙo masa ina tayar da jijiyar wuya. Bai biye mini ba sai ya yi ƙasa da murya ya ce, “Mayar da makaman hajjaju, abin ba na faɗa ba ne, na yarda za ki je amma batun anko ki ajiye shi, kina da kaya ɗinkakku wanda ba ki taɓa sawa ba sun fi kala goma.”

Habawa! Ai sai na ƙara yin sama tamkar wutar da aka watsawa fetur, sababi ba irin wanda ban yi masa ba. Da ya gaji da tsiwar tawa sai ya bar mini gidan ya fice.

Yamma ta yi, ya dawo da sallama ya shigo, ban amsa masa ba har ya iso falo ya zauna ban dubi inda yake ba bare na yi masa sannu da zuwa, wayata kawai nake latsawa.

“Ba ki ji sallama ba ne?” Ya tambaya.

A wulaƙance na ba shi amsa da cewa, “Na ji, sai aka yi ya ya?” Shiru ya yi bai ce komai ba tsawon mintuna, sannan ya sake magantuwa, ” Tashi ki kawo mini abinci.”

“Ba ka da hannaye? Ko kuturu ne kai?” Na faɗa raina a ɓace.

Wani kallon mamaki ya tsare ni da shi tare da cewa, “Maryam shin kin san wa kike faɗawa wannan maganar?”

“Waye kuwa wanda ya wuce kai Isma’il, shin akwai wani aibu a cikin maganata don na ce ka girka abin da za ka ɗurawa cikinka?

Ya girgiza kai yana faɗin, “Ya yi kyau! Ba shakka aiki yana kama da mai shi. Kara da kiyashi ɗaukar marar sani.” Yana faɗa ya wuce ɗakinsa.

Mako guda muka shafe cikin zaman doya da manja. Bayan wannan matsalar ta kau haka na riƙa kawo masa shashashan buƙatu da fituntunu kala-kala, ya yi duk mai yiyuwa wajen ganin ya nusar da ni yadda rayuwar aure take, amma na toshe kunnuwana. Wanda ya yi nisa ba ya jin kira.

Da ya ga abin nawa ba ƙarewa zai yi ba, wai kukan aure da salati. Sai ya fara gabatar da ƙorafina ga magabatana. A karon farko aka yi mini faɗa tamkar abin ya shiga kunnena amma a banza, wai an yakushi kakkausa. Ba a ci Talata ba bare Laraba na sake bijiro masa da wata ƙazamar buƙatar, akan lallai sai ya canja mini waya sabuwa ‘yar yayi.

Kai tsaye ya ce ba zai sauya ba, na riƙa faɗin, “Wannan ai zalunci ne ka ajiye ni kuma ka ƙi biya mini buƙatuna, idan ba za ka iya ba ka sawwaƙe mini na samu wanda zai yi mini komai. Aurenka ƙaddara ce mummuna a gare ni.”

“Na sake ki saki ɗaya!” Ya furta cikin kakkausan harshe.

Tsalle na yi ina faɗin, “Ta fi nono fari. Na jefar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda.”

Nan take na tattaro na dawo gidanmu, tsangwamar duniya babu irin wacce ba na gani daga wajen mahaifiyata. Har na gama iddata ban ga ƙeyar Isma’il ba, gabaɗaya zaman gidan ya ishe ni. Rana zafi inuwa ƙuna!

Na riƙa roƙon Allah Ya karkato hankalin Isma’il kaina, domin har bayan iddar tawa ko kare bai tako ƙofar gidanmu da sunan zawarci ba. Shekara ɗaya da rabi ina gida cikin damuwa, watarana na ɗauki waya na tura wa Isma’il saƙo kamar haka, “Don Allah idan ka samu lokaci ka zo Baffa yana son ganin ka.”

Ƙasa minti ɗaya da tura saƙon na ji wayata ta fara ruri, gabana ya yanke ya faɗi ganin lambar Isma’il. Ta yi ruri ta yanke, ya sake kira har sau uku na gaza ɗagawa. Domin tunda muka rabu bai fi kwana talatin ba na kira shi ya fi sau goma a lokaci guda amma bai amsa ba. Saƙon kar-ta-kwana kuwa ban san adadin da na tura masa ba. Da ya ga ba ni da alamar amsa kiran sai ya turo saƙo, “Zan zo bayan sallar Isha’i.”

Ina gama karantawa, na lumshe idanuna ina jin sanyi na ratsa farfajiyar zuciyata wacce ta rikiɗe zuwa sansanin ƙunci. Kamar yadda ya ce, bayan Isha’i ya zo, kafin mu shiga na fara ba shi haƙuri sannan na faɗa masa gaskiya kirana ne ba na su Baffa ba. Ya haƙura kuma ya amince zai mayar da ni, aka tsayar da mako mai kamawa za a sake sabon ɗaurin aure.

Bayan na dawo gidansa yake faɗa mini cewa zai yi aure, da ma bayan rabuwarmu yana neman auren ‘yar ƙanen babansa. Mai hali ba ya fasa halinsa, nan fa na sake yin tsalle na dire na ce bai isa ba. Tunda yana neman aure sai ya sanar da ni, na haƙura. Rikici sosai na kwance har gaban iyayena, ya yi bayanin komai. Baffana ya miƙe ya shiga ɗaki kamar zai ɗauko wani abu, yana fitowa na fara jin saukar dorina a jikina ya zane ni tas. Da kyar Isma’il ya karɓe ni.

“Idan har ta sake yin wani abu makamancin wannan ka sanar da ni.” Cewar Baffa ke nan yana huci.

Haka muka dawo gida, sai da na shafe wata guda ba na yi wa Isma’il magana. Ranar da ya tare da amaryarsa, ya tara mu yana mana nasiha. Zuciyata tuƙuƙi take kamar za ta hudu ƙirjina. Sautin kalmominsa kawai nake ji amma ba na iya fahimtarsu. Ban san lokacin da tunanina ya gushe ba, na cakumi amaryar na haɗa goshinta da teburin gilashin da ke gabanmu, nan take jini ya wanke mata fuska. Na zabura zan tsere, ya fizgo ni yana faɗin, “Sai dai ku yi jinyar tare, zan nuna miki ke ƙaramar marar kunya ce. Na sake saki uku!”

Ya falla mini wani gigitaccen mari wanda ji da ganina suka ɗauke na wucin-gadi, ya ci gaba da dukana, ban san me ya sake faruwa ba sai yanzu da na farka da tsintar kaina a kwance a asibiti.

Bayan na warke an sallame ni, na koma gidanmu, baƙin cikina ya kai Innata kushewa. Rayuwa ta dagule mini sosai, babu namijin da ke zuwa wajena da sunan neman aure. Sai da na shafe shekara goma ina ƙasa, girma ya fara bayyana ƙarara a jikina, ana haka shi ma mahaifina ƙasa ta rufi idonsa.

Daga ƙarshe dai na samu gidan wasu masu farcen susa nake musu wankau da wanke-wanke.

AL’UMMATA

AL’UMMATA

Kwazazzabai haɗi da ramukan da suka cika hanyar da ta zama tamkar sansanin kurege, baya ga nisan da ke tsakanin garin Malamawa da cikin gari sun isa su tabbatar da cewa mahukunta sun manta da al’ummar wannan yanki. Mun shafe kusan awanni biyu cir muna tafiya, tamkar tafiyar jefar da ɗan shege. Ga tayoyin Amalanken babu iska a ciki, ga tsananin rana da ake zubawa.

Hansatu ta gama galafaita; tun tana iya yin salatin har bakinta ya mutu, sannan ga jinin da yake ta kwaranya ta gabanta. Kafin mu samu motar da za ta ɗauko mu zuwa babban aisibitin cikin gari, mun ɓata mintuna aƙalla arba’in. Wata mota ce irin wacce ake kira Malam-Kalli-Malam, ta yo dakon itace, muka tsayar da ita. Ba mu da wani zaɓi kasancewar babu tabbas ɗin za a sake samun wata, haka nan aka kinkimi Hansatu aka shimfiɗa buhu aka ɗora ta bisa  itacen nan, duk ramin da motar ta faɗa ita ta san azabar da take ji a ranta.

Tafiya muke yi amma gani nake tamkar a waje guda muke, sakamakon laftun kayan da motar ta ɗauko sannan kuma ta tsufa matuƙa. Bayan kamar awa guda muka iso cikin gari, Adaidaita Sahu muka tara zuwa aisibitin. Mutane ne jingim masu larurori iri-iri, sun yi wa aisibitin cikar kwari, babu masaka tsinke. Ganin yanayin da Hansatu take ciki ya fi tayar da hankali sama da sauran marasa lafiyar, ya sa aka yi saurin kai ta ɗakin duhu. Ta zubar da jini sosai, ba za ta iya haihuwa ba sai an ƙara mata jini. Nan take aka gwada na ‘yan uwa da muka tafi da su, amma ba a samu koda wanda za a yi musaya da shi ba.

Wani sabon tashin hankalin ke nan da ya ƙara ɗugunzuma ni, neman jini muka fara ruwa a jallo. Likitan da ke aikin ya kira wani abokinsa da yake aiki a wani aisibitin kuɗi a birni, ya tambaye shi ko akwai jini na sayarwa? Cikin sa’a ya ce akwai. Nan ya yi mini kwatancen asibitin, nan da nan na yo wa birnin dirar mikiya, da tambaya na isa asibitin. Dayake sun riga sun gama magana, kuɗin kawai ya faɗa mini, sai dai abin cikas kuɗina naira dubu goma ne suka rage, ga shi kuma jinin naira dubu sha biyar ne, haka nan ya cika mini kuɗin har ma ya ba ni kuɗin motar da zan koma.

Isowa ta keda wuya na yi tozali da yayata Habiba a tsaye gindin wata bishiya, fuskarta murtike tamkar ba ta taɓa yin fara’a ba. Shirun da ta yi da rashin motsawa daga wajen, da abin da fuskarta ke bayyanawa suka sa jikina ya yi sanyi. Cikin ƙarfin hali na ce, “Ya ya mai jikin?”

Hawaye ne suka cika mata idanu nan take suka fara zarya a kan kuncinta. Yanayinta ya sauya, ta gama isar mini da saƙon mutuwar Hansatu. Wuce ta na yi na shigo cikin asibitin, ƙannen Hansatu guda biyu, Hauwa da Lantana na iske su ma suna ta ɓarin hawayen.

“Allah Ya jiƙan ki Hansatu, Allah Ubangiji Ya karɓi shahadarki, na yafe miki duniya da lahira!”

Abin da na furta ke nan na juya, da kyar ƙafafuwana ke ɗauka ta, ban san lokacin da ledar jinin da ke hannuna ta faɗi ba. Gindin wata itaciyar ɗorawa na jingina, duk yadda na so na hana dirar hawaye, abin ya gagara. Ɗumin hawayen na ji yana ratsa kuncina, mintuna kamar biyar ina kwaranyar da zafafan hawaye, kafin daga bisani zuciyata ta shiga hakaito mini irin tarin matsalolin da garin Malamawa ke fuskanta haɗe da adadin matan da suka rasa rayukansu akan gwiwa a hanyar zuwa aisibiti saboda rashin kyan hanya. A hannu guda kuma na tuno alƙawarin da shugaban ƙaramar hukumarmu mai-ci ya yi mana lokacin da yake neman ƙuri’unmu.

“Ni Hassan Ɗan Tambai, na yi alƙawari zan gyara muku hanyar zuwa cikin gari, zan gina babban aisibitin kula da mata masu juna-biyu da ƙananan yara. Hakazalika zan kawo ababen more rayuwa kala-kala.”

Rufe bakinsa ke da wuya, mahaifina Malam Liman, wanda ya kasance babban limamin garin namu, ya kada baki ya ce,  “Muna godiya, Allah Ya dafa maka, muna fatan ka bambanta da waɗanda suka gabace ka, ka zama zakaran gwajin dafi.”

“In Sha Allah!” Dukkan mutanen da ke wajen muka amsa.

Bayan an yi zaɓen, cikin yardar Allah, Ɗan Tambai ya samu nasara. Bisa al’ada, shi ya kamata ya sake dawowa ya yi godiya ga jama’ar da suka kaɗa masa ƙuri’a, amma ko ƙeyarsa ba mu gani ba. Wannan abu ya fara saka shakku a zukatanmu. Wata ranar Juma’a Malam Liman ya jagoranci tawagar manyan gari zuwa gidan shugaban ƙaramar hukumr domin taya shi murnar nasara, sannan kuma a tuna masa da alƙawuran da ya ɗauka. Musamman samar da asibiti a garin Malamawa. Nan ya fito aka gaisa a tsaitsaye, ya ce, “Ina mai ba ku haƙuri, kun zo ina da uzurin taro a can shalkwata, wani lokacin kun dawo.”

Bai jira wani ya yi magana daga cikin tawagar ba ya koma ciki abinsa. Kowa ransa ya ɓaci matuƙa, musamman Malam Liman, wanda hakan ya yi sanadiyar tashin hawan jininsa. Haka muka dawo gida gwiwa a saluɓe.

Wasa-wasa sai jikin Malam Liman ya fara tsananta, mun yi duk ‘yan dabarun da muka saba yi idan ciwon ya motsa amma abin sai gaba yake kamar wutar daji.

Ban daddara ba, na sake wankar ƙafa na koma gidan shugaban ƙaramar hukumar domin ya taimaka mini a kai Malam babban aisibitin a birni a duba shi. Abin takaici, bayan na yi masa bayani sai ya shiga gida ya ɗauko naira dubu biyar ya miƙo mini tare da cewa, “Ga wannan ku je ku kai shi asibiti, Allah Ya ba shi lafiya.”

Zuciyata tafasa ta riƙa yi mini, wani malolon baƙin ciki ya tokare mini ƙirji, ban san lokacin da na bar shi a wajen ba na yi ficewata. Sati ɗaya da faruwar hakan, Allah Ya karɓi rayuwar Malam.

“Ka yi haƙuri, ba kuka za ka yi mata ba, addu’a za ka yi wa Hansatu, Allah Ya jiƙan ta ya yi mata rahama. Allah Ya sa bakin wahalar ke nan!”

Yayata Habiba ce ta furta wannan maganar da ta katse mini wancan dogon tunani da na tafi, hawaye na share daidai lokacin an gama hada Hansatu. Na fito na samu mota ƙirar taxi ta ɗauko mu har gida. Aka yi jana’izar Hansatu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Ranar addu’ar bakwai, bayan an yi addu’a, na miƙe cikin taron jama’a na gabatar da kudurina na neman shugabancin ƙaramar hukumarmu kamar haka;

“Assalama Alaikum jama’a! Duk wanda ke wannan waje ya kwana da sanin yadda ‘yan siyasa suke neman ƙarar da al’ummar Malamawa! Wannan gari namu babban gari ne mai tarin jama’a amma idan muka zauna muka zuba ido, to watarana za a wayi gari sai dai a ce an taɓa yin wata al’umma mai suna MALAMAWA. Ina son ku ba ni haɗin kai da addu’a, In Sha Allah zan yi duk mai yi yuwa ni da ku mu haɗu mu fitar da A’i daga rogo.”

“Ka taɓo mana inda ke mana ciwo, da ma abin da ke ranmu ke nan! In Sha Allah za mu ba ka dukkan wani ƙwarin gwiwa da goyon baya, Allah Ya taimaka mana!”

Magajin Malam Liman ne ya yi wannan maganar wacce ta samu yardar kowa a wajen, addu’o’in fatan alkairi mutane suka ci gaba da yi.

Shirye-shirye muka fara  muka shiga siyasar sosai, cikin yardar Allah kuma aka yi zaɓe. Sabuwar jam’iyyarmu ta yi nasara, aka rantsar da ni. Cikin shekaru biyun farko al’ummar garin Malamawa suka manta da kusan kashi saba’in na matsalolin da suka yi musu ƙawanya!

Ƙarshe!

Ameera Garba

08163478965

Lafazi Writers

KYAN ƊAN MUCIJI (Gajeren Labari)

Shekarunta na tsakanin goma sha shida zuwa sha takwas, ba ta da jiki sosai, irin matan nan ne masu kirar kalangu. Fara ce matuka gaya kamar a taba ta jini ya fito, idanunta dara-dara, hanci  har baka. Gashin kanta baki wuluk, ya bayyana daga baya kasancewar ta yi daurin kallabin nan “Ture-ka-ga-tsiya!”

“Tsarki ya tabbata ga Sarkin da ya halicci kukanmu Adamu ba tare da ya kwaikwayi wani ba!”

Bakina ya furta lokacin da na isa daf da wannan zinariyar yarinya. Juyowa ta yi da irin lallausan murmushin da yake kashe Ilahirin gabobin jiki, nishadi marar misaltuwa na ji ya gauraye farfajiyar birnin zuciyata. Nauyayewa labbana da harshena suka yi, sai na tsinci kaina da zama kurma, illa fuskata da ke bayyanar da sakon zuciyata.

Ta ci gaba da takunta a nutse. Zuciyoyi biyu suka shiga turo mini shawarwari mabanbanta.

Daya daga ciki ta ce, “Kai dai ka cika namijin zara wallahi, ka ki ka tsayar da kafarka waje guda. Duk zukekiyar yarinyar da ka yi tozali da ita sai ka ce kana so. To ka saurara ka ji, irin wadannan yaran tsala-tsala da kake gani kamar su suka kagi kansu, kara da kiyashi ne daukar marar sani. Ka yafa wa kanka bargon sutura ka tsaya ga Mariya, idan ka ki ji, ba za ka ki gani ba, za ka yi nadama marar amfani.”

Dayar kuwa ce mini ta yi, “Tsaya kallon ruwa kwado ya maka kafa! Wannan gurguwar shawara ce, kada ka bar wannan ‘yar gwal din ta wuce ka. Ita ce daidai da kai. Kowacce kwarya da abokin burminta ne. Duba ka gani, yarinya marar girman kai, ga kyau da diri. Ko cikin Larabawa da Indiyawa samun irin ta sai dace. Matsa ka yi mata sallama za ku daidaita.”

Na tattaro dukkan murmushi da fara’ata na malala a annuriyar fuskata. Cikin nutsuwa na bi bayanta, “Assalama Alaiki!”

Da martanin murmushin ta juyo cikin zazzakar murya ta amsa, “Amin wa alaikas-salam!”

Na yi gyaran murya na ce, “Ki yi hakuri, na tare ki a hanya. Na san hakan bai dace ba, zan so ki yi mini alfarmar abu biyu cikin ukun da zan tambaya.”

“Hmm! Ba komai ina jin ka.”

“Na gode! Ina son ki ba ni adireshin gidanku ko kuma lambar wayarki.”

A saukake ta ce, “Ka sa 09078486874, a Sagagi nake, gida mai bishiyar dirimi.”

“Na gode! Sunana Sadik, sai kin ji ni.”

“Ni kuma Rukayya.”

Misalin karfe goma na dare, na makare wayata da kudi, na shige daki na garkame sannan na jefar da hakarkarina bisa shimfida, na lalubi lambar da na yi sebin da “ZABINA NA KARSHE.” Bugun farko ta shiga, aka daga da cewa, “Hello!”

“Barka da dare!” Na fada ina shafa kirjina.

“Waye?”  Ta tambaya.

Murmushi mai sauti na saki sannan na ce, “Sadik ne, wanda kika bawa lamba dazu a titin gidan Zoo.”

“Okay, ya kake?”

“Lafiya kalau da fatan kin isa gida lafiya?”

“Lafiya kalau!”

Cikin makwanni biyu muka fahimci juna, muka sasanta kanmu. Na nemi damar gabatar da magabatana, ta amsa mini ba tare da wani jinkiri ba.

To kalubalena a yanzu shi ne yadda zan rushe baikona da Mariya, wacce ita ce budurwa ta biyar da ake mini baiko daga baya na fitittike na ce ban san zancen ba. Dalilin haka yasa Alhajinmu ya dawo daga rakiyata. A cewarsa ba zan rika zubar masa da martaba ba. Don haka ban tunkare shi ba, wajen kanensa na nufa, shi ya ci gaba da daure mini gindi.

Ya wanki kafa ya je wajen magabatan Mariya, ya shirya musu karyar cewa wai karatu zan tafi kasar waje. Daga karshe ya ce duk abin da aka kai da kudi a bar wa yarinya. Bayan wannan kuma na tura shi gidan su Rukayya domin ya nema mini aurenta.

Watanni biyu na bukaci a saka bikin, kafin cikar wa’adin mun kara shakuwa sosai da Rukayya, ta iya kalamai masu tsada na soyayya, ga kwalliya tamkar digirin-digirgri ne da ita a fannin. Wadannan siffofi nata suka kara mini kaunarta, sannu a hankali ranar biki ta zo, aka yi kasaitaccen shagalin da na fesar da da masu gidan rana tamkar ruwan sama.

Sati guda da tarewarmu na da dawo daga kasuwa da wasu kudaden cinikin kaya naira dubu maitan. Washegari da safe zan fita, na dauki kudi na ji nauyinsu ya ragu. Kirgawa na yi, naira dubu (150,000) na gani. Na tisa kidayar kudin nan har sau uku. Na dubi Rukayya na ce, “Abin mamaki rakumi cikin kuratandu! Kin ga na zo da kudi naira dubu (200,000) amma babu dubu hamsin.”
“Anya kuwa ka lissafa da kyau, mu gani.”
Ta karba ta sake tisa su sannan ta ce, “Watakila dai hakan ka zo da su, ka tuna.”
Ban yi gardama ba na karba na fice. Duk lokacin da zan zo da kudi sai na ga wasu sun zame, abin na matukar ba ni mamaki, batan nono a kirjin budurwa. Ban yi zargin Rukayya ba da farko, amma da na fuskanci abin zai wuce makadi da rawa, sai wata dabara ta zo mini. Idan na zo da kudi sai na ba ta ajiya.
An ki cin biri an ci dila! Hakan ma ba a tsira ba. Watarana na zo da naira (300,000), na ba ta ajiya. Da safe aka yi mini wayar gaggawa na karbi kudin na fita, a kasuwa na kwance kudi ina kirgawa, naira dubu dari biyu na gani. Na ciji yatsa, raina ya yi matukar baci.
Da marece na dawo na ce mata, “Kudin nan da na ba ki, babu naira dubu dari, ni fa abin nan ya fara isa ta, gida mu biyu amma a rika samun batan kudade.”
Ta bata rai, “To ko zargi na kake yi?”
“Ni ba haka nake nufi ba amma abin da mamaki sarki gwauro talaka da mata hudu.”
“Ka ga malam ka fito fili ka ce ni barauniya ce, ka daina noke-noke.”
“Wannan ke kika fada, ni ban ce miki barauniya ba.”
Kuka ta saki, ba yadda na iya haka na rarrashe ta. Matakin karshe da na dauka shi ne, daina zuwa da kudaden gida, iyakacin wadanda za mu amfani da su nake daukowa. To su din ma ba su shallake ba, haka na rika ganin gibi.
Rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya. Wannan magana tamkar nassi haka take, a wata Asubar Laraba,  na fito zan tafi Masallaci karaf idona ya yi tozali da Rukayya rike da wandona, hannayenta dumu-dumu cikin aljihu.
A bahagon tunaninta na riga na fita, tsuru-tsuru ta yi, ta rasa inda za ta buya.
“Alhamdu Lillah!” Na fada sannan na fice.
Ana sallamewa daga salla na taso, a raina na ce, “Ashe da ma duk ta’asar da ake mini Rukayya ce? Biri ya yi kama da mutum! Kyanki ya zama KYAN DAN MUCIJI, Sata mugun aiki!”
Wajen da na bar ta na iske ta tana zubar da hawaye, cikin kukan ta ce, “Don Allah ka yi hakuri, na butulce maka duk da irin kulawar da kake ba ni. Sharrin shaidan ne, ka yafe mini ba zan sake ba.”
Tausayinta ya kama ni, “Na yafe miki, Allah Ya shirya ki, Ya ganar da ke.”
Kimanin wata guda babu abin da ya sake zamewa a kudin da nake zowa da su, hakan ya sa na ci gaba da kawo kudin ciniki, yadda na shigo da su haka nake fita da su ko anini ba ya bata. Na yi matukar jin dadin hakan.

Bayan Wata Uku

Watarana muna zaune a falo sako ya shigo wayarta, ta karanta. Sai na lura yanayinta ya sauya. Mikewa ta yi ta shiga bayi rike da wayar, mamaki ya kama ni kamar zan yi magana sai na yi shiru. Ta jima a bayin sai na gaza hakuri, na tashi na je wajen na tsaya.
Abin da na’urar isar da sautina ta ji ya fara sauya yanayina, “Haba baby ka yi hakuri, tunda na ce sai goben ai zan zo. Yau maigidana ne bai fita ba, kuma fa kai ma ba ka cika alkawari ba, ba ka turo mini kudin ba har yanzu.”
Ta yi shiru, alamar tana sauraren abin da yake fada mata, zuwa can ta ce, “To shike nan zan turo maka sabon bidiyona mai zafi, za ka ji tamkar muna tare.”
Kafafuwana na ji suna shirin gaza dauka ta, duhu-duhu ya fara rufe mini maganaina. Da kyar na komo falo na zauna, mintuna kamar biyu sai ga ta ta fito. Ban tsaya wata-wata ba na mika hannu cikin tsawa na ce, “Ba ni wayarki!”
Jikinta ya hau bari, saboda tsananin razana wayar ta subuce, muka yi wawaso ni da ita, Allah Ya ba ni sa’a na dauke ta sannan na falla mata kyakkyawan mari sai da ta tintsira.
Na shiga binciken wayar, bidiyoyinta na tsiraici da sakonnin batsa da sakonnin karta-kwana na banki da ake turo kudade. Kaina ya sara sau uku a jere.
“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!” Jimlar da na rika maimaitawa ke nan, Ubangiji Ya agaza mini yanayina ya dan saitu.
“Na sake ki Rukayya saki daya!”
Babu shakka hakkin ‘yammatan baya da na yi wa wulakanci ne ya kama ni, Allah Ya yi mini zabin alkairi amma na butulce, na biye wa KYAN DAN MUCIJI!

Karshe!

TSININ HARSHE YA FI NA MASHI

➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶
❝ᴍᵃⁿᶻᵒⁿ ᴀˡˡᵃʰ (sᴀᴡ) ⁿᵃ ᶜᵉʷᵃ, ”ʟᵃˡˡᵃⁱ ᵇᵃʷᵃ ʸᵃⁿᵃ ᶠᵃᵈⁱⁿ ᵐᵃᵍᵃⁿᵃ ᵗᵃ ᵏᵃˡᵐᵃ ᵈᵃ ᶻᵃ ᵗᵃ ˢʰⁱᵍᵃʳ ᵈᵃ ˢʰⁱ ᶜⁱᵏⁱⁿ ʷᵘᵗᵃ, ᵗᵃ ᵏᵃⁱ ˢʰⁱ ⁿᵉˢᵃⁿ ᵈᵃ ʸᵃ ᶠⁱ ⁿⁱˢᵃⁿ ᵗˢᵃᵏᵃⁿⁱⁿ ᵍᵃᵇᵃᶜⁱ ᵈᵃ ʸᵃᵐᵐᵃᶜⁱ.”❞
➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶➶

ᴛsɪɴɪɴ ʜᴀʀsʜᴇ ʏᴀ ғɪ ɴᴀ ᴍᴀsʜɪ ➶➶➶
(Gαյҽɾҽղ Lαճαɾí)

Sɑdik Abubukɑr
LAFAZI WRITERS
Wɑttpɑd @sɑdikgg

Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

“Na tabbatar da ke Jummai ta yi wa shaƙar da ta yi mini, da yanzu ba wannan maganar muke ba. Wataƙila da kina can gari me arhar gyaɗa.”

“Zainab! Har kullum ina raba ki da irin waɗannan zantuka marasa kangado, za ki ɗaure kanki da kanki fa! Zargin maita da kike gani wuya ne da shi. Ki iya bakinki, ni kin ma kore ni bari na koma gidana da ma cewa na yi bari na zo mu yi hira.”

“Ai ku ba son a faɗi gaskiya kuke ba, amma waye bai san halin Jummai ba. Tani ma da tsohon cikinta haka matsiyaciyar matar nan ta riƙa wahalar da ita, da kyar ta samu ta rabu da cikin lafiya.”

“Sai anjima kin ji.” Hafsat ta faɗa tare miƙewa ta fice abinta.

“Allah Ya raka taki gona, ki fi ruwa gudu ma. Ke ni fa, ke ma ɗin nan, don dai mun haɗa jini da ke ne da sai na ce ko ‘yar uwar ɗayar ce. “


Zainab kenan da Hafsat ‘yar wan babanta. Tana zargin wata makwabciyarsu da maita. Kuma ta yaɗa zargin har cikin matan unguwar tasu sun fara yarda cewa Jumman mayya ce. Unguwar dai ta kasance ta yaran mata ce, wato mafiya yawan mazauna unguwar ba manya ba ne amare ne da waɗanda ba su haura shekara biyar da aure ba.

Ita dai wannan baiwar Allah da ake wa sharrin cewa mayya ce har ta lashi wasu a unguwar, ta kasance irin mutanen nan ne marasa son magana sannan ba ta da son shiga jama’a, shiru-shiru ce babu ruwanta da jama’a. Wannan dalili da wata sifa tata, wato tana da idanu ƙwala-ƙwala ga su jajir tamkar gautan da ya shekara a rana, su ne suka sa mutanen unguwar tasu ke yi mata wannan ƙazafin.

Sun jima suna mata wannan zargi, tun ba ta sani har ta sani; tun ba ta kulawa har ta fara jin haushin abin. Yanzu har ta kai ta kawo waɗanda ba ‘yan unguwar ba ma sun sani.

Watarana a gidan wani suna da aka yi a nan unguwar tasu, mata sun taru an cika gidan fal ana ta shagali, masu kai da kawon raba abinci na yi, masu zaman gulma na yi. Babu irin nau’in gungu na mata da babu a gidan, Zainab da ‘yar uwarta Hafsat da wasu kawayensu na zaune suna cin abinci sai ga Jummai nan ta leƙo ta taya mai jego murna haɗe da yi mata barka. Ɗago kan da Zainab za ta yi ta hangi Jummai na shigowa, daidai lokacin ta zuba lomar shinkafa a bakinta, ai ko kamar an saka injin buga iska an huro shinkafar nan, fesh, ta feshe abokan cin abincin, ta kama wani tari na munafurci tana dafe ƙirji.

“Kai Zainab mene ne haka kuma? Kamar ƙaramar yarinya ana cin abinci ki yi wannan ɗanyen aiki?”
Hafsat ce ta faɗi wannan maganar.

Yayin da Zainab ta riƙa kakarin amai na ƙarya ta ce, “Ku yi mini uzuri don Allah ba yin kaina ba ne, masu ciki biyu ne suka iso ku ma ku yi ta kanku.”

“Ba mu gane masu ciki biyu ba? Wacece mayya kuma da ta shigo har ta kama ki haka?”

Da wutsiyar ido Zainab ta nuna Jummai, wacce ta sha alwashin yau dai sai ta tanka wa Zainab ɗin dangane da jakar tsabar da take ƙoƙarin rataya mata, kaji su bi ta suna tsattsaga. Gabaɗaya mutanen da ke wajen suka jiyo da kallon mamaki ga Jummai, ƙarasawa ta yi tana cewa, “Yau sai kin nuna mini maitar da kike zargina ko kuma ki fito da wanda na taɓa ci. Na gaji da wannan renin wayon naki, ni ba shiga sabgarki nake ba. Ke ba ke ba shashasha ma, waɗanda suka fi ki nutsuwa ma ba shigar harkarsu nake ba. Don haka wallahi yau ɗin kin yi na farko kin yi na ƙarshe, ba sharrin maita ba kowanne irin sharri ne kin daina yin sa, za a koya miki yadda rayuwar duniya take.”

A fusace Zainab ta miƙe tsaye tare da hayayyaƙo wa Jummai tamkar za ta haɗiye ta tana faɗin, “Ke dalla garafara can mayyar banza mayyar wofi, yo waye bai san wannan mugun halin naki ba. Ke nan har kina da bakin magana, lallai rashin kunyar taki ta gawurta. To bari ki ji, da dai kin wahalar da ni, amma yanzu ba ki isa ba kurwata ɗaci gare ta.”

“Kada ki ƙara kira na da mayya.”

A zafafe Zainab ta dangwale wa Jummai hancin tare da cewa, “An kira ki mayyar, me za ki yi, ƙarya ake yi ne?”

Kafin ka ce me ita ma jumman ta mayar mata da martanin dangwale hancin, nan fa kokawa ta kaure tsakaninsu duk da cewa sauran mutanen da ke wajen sun yi ta ba su baki akan su bari amma sun ƙi. Nan da nan gidan ya yamutse hayaniya kawai ke tashi wani baya gane abin da wani yake cewa. Jummai ta riƙe Zainab gam sai jibga take kamar Allah Ya aiko ta; da kyar mutane suka raba su. Haki kawai Zainab take, ta gaza magana ta daku sosai.

Gidan suna ya hargitse, kafin kiftawar ido masu ƙaramar zuciya har sun fara halin nasu. Cigiyar wayoyi aka fara, daga wannan ta ce ina wayata? Sai ka ji wata ma ta yi makamancin wannan tambayar. Me jego ta fito ba da haƙuri kafin ta koma an ɗauke jakar da take tara kuɗin gudummawar da abokan arziki ke kawo mata, mutum biyar aka sacewa waya a ɗan taƙin da bai wuce mintuna biyar ɗin ba.

Nan fa kiɗa ya sauya, waɗanda aka yi wa sata suka yi tsalle suka dire suka ce, Allah Ya kashe su ya rufe ba za su ɗauki ƙaddara ba, Zainab ce ta haddasa fitinar da aka yi musu satar don haka sai an fito musu da wayoyinsu. Komawar da Me jego za ta yi ɗaki ta ɗauko wayarta domin a kira wayoyin da ba a gani ba, jaka ta ce, “Ɗauke ni inda kika aje.”

A tsakar gida kuma mata ne suka yi ram da Zainab wasu na cewa, “Da haɗin bakinta aka yi musu satar, ita ta zo da ɓarayin don haka lallai ta fito musu da wayoyinsu.”

“Ke wallahi ba ki isa ba ki raina mana hankali kin ji, idan kina son hukuma ta raba mu to kada ku fito mana da wayoyinmu.”

Wata ke nan cikin waɗanda aka sha basilla. kafin ka ce kwabo, zufa ta karyo wa Zainab ta rasa wa za ta saurara bare har ta iya cewa wani abin, daga wannan ta rufe bakinta sai wata ta ɗora, haka dai ake ta yi mata gayyar haƙori.

“Tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan doka.”

Hafsat ta faɗa daidai lokacin da Me jego ta fito daga ɗakin tana sallallami, “Me ya faru Fatima?”

Wata cikin matan ta tambaya a kiɗeme, yayin da sauran jama’a suka watso hajjar mujiyarsu kan Fatima, wato Me jego.

“Ku taku satar me sauƙi ce, ni gabaɗaya an ɗauke mini jakar, wayata da kuɗin Abban Ilham dubu ɗari biyar (₦500,000) a ciki da ya ba ni na ajiye masa ranar Litinin zai karɓa.”

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN!”

Mafi yawan matan suka furta cikin sigar razani haɗe da zaro idanu, wata ta ɗora da cewa, “A garƙame gidan nan kawai babu wacce za ta fita sai an caje ta tsaf har ɗan kanfai.”

“E, haka za a yi, haka za a yi.” Suka faɗa a tare, sai dai kash! Kafin tunanin hakan ya zo, tuni wasu mata biyu da ba me iya tantace su suka yi layar zana daga gida n. Wata cikin matan ta ce, “Babu wani caje da za mu tsaya yi mu ɓata wa kanmu lokaci, ga wacce ta zo da ɓarayin nan.” Ta nuna Zainab haɗe da wani irin mugun kallo tamkar ta kashe ta, sannan ta ci gaba da cewa, “Ni caji ofis kawai zan je ɗauko mata Ɗansanda, wallahi sai an biya ni wayata. Ko wata guda ba ta yi ba, Abban Islam ya sayo mini kuma ya gargaɗe ni akan ko gilashin ne ya fashe sai raina ya ɓaci, bare kuma na ce masa an sace. Sam ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa.”

Tana faɗa ta fice, ta nufi wani ɗan ƙaramin caji ofis da ke kusa da gidan sunan, ta shiga kai tsaye ta nufi kan kanta ta yi ƙorafin cewa ta kawo ƙarar zargin wata mata ta yi sanadin sace mata waya, ba ita kaɗai ba har da wasu. Nan take aka hada ta da ‘Yansanda biyu, mace da namiji. Suna zuwa, sauran matan suka ce “Kin yi daidai wallahi gara da kika kawo hukuma, domin an caje kowa ba a ga koda waya ɗaya ba. Su hukuma sun san yadda za su ɓullo wa lamarin.”

“Ya isa haka, ya isa.” Jami’ar ‘yarsandar ta faɗa tare da duban wacce ta kai ƙarar ta ce, “Wace ce ake zargi da tayar da hatsaniyar?”

Ta nuna Zainab, tare da cewa, “Ga ta nan ranki yadaɗe.”

Zainab tuni ido ya raina fata, ta yi tsuru-tsuru da ita, yau fa ake yin ta, lallai baki shi ke yanka wuya. Allura ta tono garma. “Baiwar Allah ɗauki mayafinki mu je.”

‘Yarsanda ta faɗa, sai yanzu ne zai ta buɗa baki ta ce, “Don Allah ki yi haƙuri, ni wallahi babu ruwana, da wannan muke rigima ne.”

Zainab ta faɗa tare da nuna Jummai, ‘yarsandar ta ce, “Idan mun je can za ki yi bayanin komai.”

Nan dai aka tisa ƙeyar Zainab zuwa ofishin ‘yansandan, sauran waɗanda aka yi wa satar da me jegon su ma suka rankaya gabaɗaya domin neman hakkinsu. Suna isa aka rubuta jawabi duk yadda aka yi. Dayake ƙaramin ofishin ‘yansanda ne, me mukamin DCO ne ke shugabantar wajen, shi ne kuma ya karɓi ƙorafin. Bayan ya ji ta bakin masu korafin sai ya dubi Zainab ya ce, “Garin ya haka ta faru? Ina kayan da ake zarginki da su?”

“Yallaɓai, ni wallahi ban san komai ba game da wayoyinsu, hasalima ma ni a gefe guda nake. Cacar ba ki muka yi da wata kawai shi ne suka fara cigiyar wayoyin.”

“Da ma ba su ce ke kika dauka da hannunki ba amma suna zargin kin haɗa baki da wasu, yayin da kika tada hatsaniyar ke da waccan matar, su kuma suka yi hauzi da wayoyin.”

Me jego ta ce, “Ranka yadaɗe, ba fa wayoyi kawai aka sace ba, har da jakata akwai kuɗin megidana dubu dari biyar (₦500,000) a ciki da wayata duka an yi gaba da su.”

Yallaɓai ya jinjina kai alamar al’amarin babba ne, nisawa ya yi sannan ya ce, “Za mu tsare wacce ake zargi mu faɗaɗa bincike domin a yi wa kowa adalci, kafin nan kowacce ta zo da megidanta ke ma wacce ake zargi za ki kira megidanki ko mahaifinki ko yayanki.”

BAYAN MAGARIBA

A ɗan taƙin da ke tsakanin Magariba da Isha dukkan mazajen waɗannan mata suka dawo daga wajen neman na Masara, ita kuwa Zainab da ma tun tuni mahaifiyarta ta je ofishin ‘yansandan bayan da ‘yar uwarta Hafsat ta sanar da labarin. To sai dai duk da zuwan mahaifiyar tata ba a sake ta ba sakamakon masu ƙorafin suna gida, don haka ita ma sai DCOn ya ce ta koma sai lokacin da sauran masu ƙorafin suka dawo za a ci gaba da sauraren ƙarar.

To mutum biyu daga cikin mazajen matan ƙin zuwa ofishin ‘yansandan suka yi, guda ya ce, ba zai je ko’ina ba kuma ba sake saya wa matar waya ba, da ma ba wannan ne karo na farko ba da ta saba yin wasarairai da wayar ana sacewa. Don haka ta saya da kuɗinta. Gudan kuwa cewa ya yi, shi kenan ya yafe wa duk ma wacce ta ɗauka, indai waya ce zai saya wa matar wata.

Mijin me jego da aka fi targaɗawa da sauran mazan da ba za su haƙura ba, su suka halarci ofishin ‘yansandan, bayan an sake bayanin yadda abin ya kasance, Zainab ba ta musa ba, a nan mahaifiyarta ta rufe ta da faɗa, babban yayanta ma sai fadan yake mata. Yallaɓan ya ce, “A iya abin da bincike ya nuna, ba a samu fara cigiyar wayoyin ba sai da Zainab ta tayar da hatsaniya tsakaninta da wacce take wa zargin maita, don haka a nan dole ta ɗauki alhakin biyan mutane dukiyoyinsu idan ba su yafe ba.”

“Zargin maita?” Mahaifiyar Zainab ta fada cikin sigar mamaki hade da zaro idanu, kafin ta ci gaba da magana mijin Zainab ɗin ya karɓe zancen da cewa, “Wallahi Umma na yi fama da ita akan ta iya bakinta, abin duk da ba ka da hujja akansa to wuyar sha’anin ne da shi, amma ba ta ji.”

A fusace Umman ta dubi Zainab da wata harara me cike da tuhuma ta ce, “Uban wa kike wa sharrin maita? Allah wadaranki Zainab!”

DCOn ya katse ta da cewa, “Ya isa Baba, ki daina furta mata irin waɗannan kalamai, tabbas za su yi tasiri a jikinta, addu’a za ku ci gaba da yi mata. Yaran zamani sai haƙuri idan muka ce za mu biye ta halinsu sai su sa mu yi musu abin da ko ƙuda ma ba zai raɓe su ba. Allah Ya shirya mana su kawai.”

Gabaɗaya suka amsa da, “Amin.”

Ya sake juyawa ga masu ƙorafi, ya ce, “To kun ga abin da ya kasance.”

Mutum ɗaya ya ce shi ya yafe Allah Ya kiyaye gaba, saura mutum biyu da kuma mijin me jego. Babban yayan Zainab ya ce zai biya naira dubu ɗari biyar ɗin da ke cikin jakar me jego da wayarta iPhone4S. Haka mijin nata shi ma ba yadda ya iya ya ɗauki gabaran biyan kuɗin wayoyi biyu. Daga karshe DCO ya yi wa Zainab cikakken gargaɗi da jan kunnen akan matuƙar aka sake kawo ƙarar ta da irin wannan ƙorafi na sata, to sai ya tura ta kotu kuma daga can gidan gyaran hali za a tisa ƙeyarta.

Kwana daya tak! Da faruwar wannan abu, Jummai ta yankowa Zainab sammaci a kotu. Ta yi ƙarar ta ne akan tana laƙa mata sharrin maita. Bayan da mijinta ya dawo ya samu labarin hakan, nan take ya yi mata saki ɗaya sannan ya ce, shi babu ruwansa ba zai iya da ita ba. Ya yi bakin ƙoƙarinsa ya ga ji.

Masifu goma da ashirin sun kewaye Zainab, ita kanta ta yi nadamar furta wa Jummai kalmar maita, idonta ya raina fata, cikin ‘yan kwanaki ƙalilan ta rame ta yi baƙi. Ta rasa farinciki da walwala, ita kanta yanzu haushin kanta take ji. Ga aurenta ya mutu ga sammacin kotu wanda ba ta da kalma ɗaya da za ta iya kare kanta da ita.

“Na shiga uku! Wai mene ne yake samu na haka? Allah na tuba ka yafe mini kurakuraina.”

Ta furta cikin sassanyar murya, wasu hawayen nadama na tsere bisa kuncinta. Hafsat da ke kusa da ita ta ce, “AlhamduLillah! Tunda har kin gano kin yi kuskure kina roƙon Ubangiji Ya yafe miki, haka ake so dama. Lokacin da idonki ya rufe babu irin hakaito miki da wannan yanayi da kika jefa kanki a ciki da ban yi ba, amma sai kika biye wa ruɗin shaiɗan da son zuciyarki, kika saka auduga kika toshe kunnenki. Don haka yanzu shawarar da zan ba ki idan an je kotu gobe, ki amsa laifinki da wuri, ki ce sharrin shaiɗan ne kina neman afuwar kotu.”

“To shi kenan na gode sosai, kuma don Allah ke ma ki yafe mini duk rashin kunyar da na yi miki, wallahi ba a hayyacina na yi ba.”

“Ki daina kuka, ba komai Allah Ya yafe mana gabaɗaya.”

“Anty Hafsat, yanzu Auwal haka zai yi mini don ya ga ina son sa?” Ta furta tana sake fashewa da kuka, rungume ta Hafsat ɗin ta yi tana cewa, “Gaskiya Auwal ya yi haƙuri da ke, ba kowanne namiji ba ne zai iya haƙuri da irin halinki, kina yawan janyo fitintunu, ba wannan ne karon farko ba. Don haka ki yi haƙuri har ya huce, ransa ne ya ɓaci amma shi ma yana son ki sosai, rashin nutsuwarki ce dai ta ja miki. Ki bari ya sakko tukunna ni zan yi masa magana.”

Washegari aka shiga kotu, bayan magatakarda ya karanto ƙarar da Jummai ta shigar bisa sharrin da Zainab take mata na maita, sai Maishari’a ya buƙaci mai ƙara da wacce ake ƙara da su fito su tsaya a ɗan kawayen da ake tsayawa yayin kare kai ko ba da hujja.

Maishari’a ya dubi Zainab ya ce, “Malama Zainabu, Malama Jummai na ƙarar ki bisa zargin kina yi mata sharrin maita, shin ko za ki iya yi wa kotu bayanin abin da kike da’awa tare da kawo gamsassun hujjoji?”

Cikin rawar murya Zainab ta ce, “Allah Ya gafarta Malam, wallahi sharrin shaiɗan ne, ni ba ma sosai muke mu’amala da ita ba. Ina roƙon wannan kotu me adalci da ta yi mini afuwa ba zan sake kwatanta irin wannan maganar ga kowa ba.”

Maishari’a ya ɗan yi shiru yana nazarin korafin da zantukan da Zainab ta yi, wato neman fitina ne kawai irin na wasu matan, ƙage ne da ƙazafi kawai. Ya ɗan gyara zaman tabaransa ya dubi Zainab ya ce, “Suka irin na harshe yana shiga da zurfi kuma yana da tasiri matsananci da ke tsayawa a zuciya. Suka irin na mashi yana iya warkewa, amma suka irin na harshe ba ya warkewa.

Harshe na’ura ne na sarrafa magana da fasaha kuma shi ke fassara abin da ke zuciya, siffarsa ɗan ƙarami ne amma sukarsa na da girman biyayya gare shi. Abu ne mai girma da laifinsa, da shi ne kafurci ke bayyana ko imani. Wanda kuma su ɗin nan su ne maƙura na ɗa’a da saɓo, yana da fage mai faɗi a. alheri, kamar yadda yake da da makamancinsa wurin girma na sharri. Da shi ne ake yaɗa tuhume-tuhume ake kuma ƙazafi ga mata katangaggu muminai, da harshe ne fitintinu da rikece-rikece ke aukuwa. Haka nan da shi ne ɓoyayyun abubuwa ke bayyana. Kuma da shi ne ake halatta abubuwa masu alfarma, kuma ake shuka fitintinu da gaba da baƙin ciki da hasara cikin zukata. Har ila yau da shi ne kuma ake zagi kuma ake yafuce ake annamimanci, kuma da zunɗe, da yaɗa jita-jita kuma da tsinuwa da cin nama da alfasha da kuma maganar banza, da batsa da suka. Harshe ba ya gajiya da motsi, kuma ba ya raguwa saboda magana, amma kuma duk da haka abu ne kiyayayye, adananne, kuma za a yi wa mutum hisabi game da shi ranan da za a yi narkon azaba.

(Harshe ba ya furta wata magana face a like da shi akwai mai tsaro halartacce)

(Watarana Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya rike harshensa sai ya ce: “Ya Mu’az ka kiyayi wannan! Sai Mu’az ya ce: Wai shin ana kama mu da abin da muke furtawa? sai Annabi ya ce: Mahaifiyarka ta yi wabinka ya kai Mu’az! Shin akwai abin da yake kifar da mutane cikin wuta a bisa fuskokinsu ko hancinsu face abin da harsunansu ke girbe musu.”

Watarana Ibnu Mas’ud ya hau kan Dutsen Safa sai ya rike harshensa sai ya ce: Ya harshe ka fadi alheri za ka samu riba, ka kame daga fadin sharri za ka kubuta tun kafin ka yi nadama. Sannan ya ce, (Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “Mafi yawan kurakuran Ɗan Adam na samuwa ne daga harshensa.””

Wannan wa’azi da jan hankali da Maishari’a ya yi, ba ga iya mai laifin ya amfanar ba, duk wani mahaluki da ya kasance a kotun ya amfana da wannan wa’azi. Sai da jikin kowa ya yi sanyi sannan ya dakata, daga ƙarshe ya umarci Zainab da ta ba wa Jummai haƙuri haɗe da neman yafiyarta, alatilas ta sauke duk wani taurin kai, ta ƙasƙantar da kai ta dube ta cikin yanayin ban tausayi ta ce, “Kin yi haƙuri don Allah, ki yafe mini.”

Zainab ta ce, “Ni na yafe miki duniya da lahira, Allah Ya yafe mana gabaɗaya.”

BAYAN SATI ƊATA

Bayan sati guda da zuwa kotu ne, sai al’amura suka fara sauya wa Zainab, zaman gidan da take yi ya fara gundurarta tun ba a je ko’ina ba. Tsangwama da tsana ta kowacce fuska, ba ga wajen mahaifinta ba bare kuma mahaifiyarta, hakan ƙananan ƙannenta suka fara raina ta, sukan faɗa mata maganar da ransu ya yi musu daɗi, ba damar ta kama su ta doka. Wannan abu ya ishe ta, rana zafi inuwa ƙuna.

Watarana sai Hafsat ta zo gidan, Zainab take faɗa mata abubuwan da take fuskanta na tsangwama daga iyayen nata. Hafsat ta yi murmushin takaici sannan ta ce, “Ke da ma kina zaton za ki samu sakin fuska kamar yadda kika samu gabanin ki bar gabansu? Ai duk macen da ta bar gaban iyayenta, to ta yi haƙuri da duk abin da ta gani a gidan miji, hakan ya fi mata gaban iyayenta nesa ba kusa, komai wahalar da take sha gidan miji ya fi gidan iyaye, bare kuma ke babu wata wahala da kike sha. Halinki ne ya janyo miki duk abin da kika gani a yau, idanunki sun makance wa gaskiya, kunnuwanki sun kurumce wa gaskiya. Duk irin jan hankali da hatsarin da ke tattare da yi wa mutum ƙazafi ba wanda ban nuna miki ba amma kika ƙi ji, yanzu kalli yadda kika koma, kin rame kin yi baƙi kin rasa nutsuwarki gabaɗaya.”

“Anty Hafsat, na yi nadama! Don Allah ki taimaka mini, ki yi wa Auwal magana ya yi hakuri na koma gidana.”

Cikin sigar kuka me ban tausayi take maganar, Hafsat ta ce, “Ki daina kuka ki shirya gobe weekend mu je gidan tare da ke, In Sha Allahu zai haƙura.”

Washegari suka shirya kamar yadda Hafsat ta tsara, suka tafi, cikin sa’a suka iske shi. Bayan sun gaisa, Hafsat ta ɗora da cewa, “Don Allah wata alfarma ɗaya zan nema a wajenka! Auwal don girman Allah ka yi haƙuri, babu shakka ka yi haƙuri da Zainab matuƙa, duk abin da ya faru a baya ya riga ya wuce, Zainab ta yi nadama ta yi alƙawarin ba za ta sake aikata wani abu makamancin na baya ba. Na kawo ta nan ta ba ka haƙuri ne da bakinta.”

“Na ji dukkan bayananki, to AlhamduLillah! Da ma ni ba rabuwa da ita na yi ba, na yi mata hakan ne a matsayin jan kunne na ƙarshe kuma na san har in ba tana da matsalar ƙwaƙwalwa ba ne, to ba shakka za ta hankaltu da wannan jan kunne. Ke shaida ce Hafsat, duk abubuwan da Zainab take ba su cika damu na ba indai ba wani ta taɓa ba, na faɗa mata ba na son tana shiga sabgar da ba ta shafe ta ba. Saboda haka na ce za ta koma makaranta, amma fur sai ta ce ita ba ta so, kada ma na yi asarar kuɗina.”

“Au haka ma aka yi? Lallai Zainab ba ki da gaskiya, to ƙaryarki ta sha ƙarya. Makaranta kamar kin koma ne, ai ni ban san haka aka yi ba. Wato saboda su sauran kawayen naki ba su samu damar yin karatun ba shi ne ke Allah Ya ni’imta ki da wanda zai ɗauki nauyinki shi za ki watsar? Maza ki ba shi haƙuri.”

Allah Sarki! Duk tsiwa da zaƙalƙalar Zainab sun ɓace mata ɓat, ta zama abin tausayi. Rayuwa ta saita mata tunani, duniya makaranta in ji masu iya magana. Nisawa ta yi za ta fara magana, Ya katse ta da cewa, “Shi kenan babu damuwa, ba komai. Zan zo gidan anjima da yammaci.”

“To shi kenan, na gode sosai Auwal, Allah Ya saka da mafificin alkairi, Allah Ya jikan magabata. Zamu koma?”

Duk da cewa unguwar ba nesa ba ne, dubu biyu ya ba su kudin mota, sun ki karɓa amma ya matsa sai da suka karɓa.

Da yammaci kamar yadda ya alkawarta musu zai zo, hakan kuwa ya yi. Ya isa misalin karfe 5:00pm, Bayan sun gaisa da iyayen Zainab ya ce ya zo ne ya mayar da ita. Daga mahaifiyarta har mahaifinta babu wanda ya ji haushin Auwal ɗin lokacin da ta zo da takardar sakin, domin sun san matuƙar haƙuri ya yi haƙuri da Zainab. Don haka sai da suka yi mata faɗa sosai mai ratsa jiki sannan suka yi musu fatan alkairi.

Zainab ta dawo gidanta, cikin ƙanƙanen lokaci jikinta ya dawo ta gyaru sosai ta yi dumurmur da ita. Sannan kuma kamar an yi ruwa an ɗauke, ta manta da duk wasu halayenta na tsokana da rashin son zaman lafiya. Yanzu tsantsar biyayya da ƙauna take nunawa Auwal dinta, jin shi take ya fi yarima ma.

Karshe!

MATAKIN NASARA 01

MATAKIN NASARA

(For indeed, with hardship there will be ease, Qur’an 94:5.)
      
Sɑdik Abubukɑr
Wɑttpɑd @sɑdikgg

PEN WRITERS.

TSOKACI

ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋᴀɢᴀɢɢᴇ ɴᴇ, ʙᴀɴ ʀᴜʙᴜᴛᴀ sʜɪ ʙᴀ ᴅᴀɴ ᴄɪɴ ᴢᴀʀᴀғɪɴ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴋᴜᴍᴀ ᴡᴀᴛᴀ ʙᴀ. ᴅᴜᴋ sᴜɴᴀʏᴇɴ ᴍᴜᴛᴀɴᴇ ᴅᴀ ɢᴜʀᴀʀᴇɴ ᴅᴀ ɴᴀ ʏɪ ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ sᴜ, ᴅᴜᴋ ʙᴀ sᴜ sʜᴀғɪ ᴋᴏᴡᴀɴᴇ ᴍᴀʜᴀʟᴜᴋɪ ʙᴀ. ✍️

Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ.

♠️Dedicɑted To♠️
              
My fɑmily, friends, fɑns ɑnd the entire world of novel reɑders, one love for you ɑll ✌

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Dukkan godiya da yabo marasa iyaka sun tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, tsira da amincin Allah su kara jaddada ga Annabi MUHAMMAD ((Sallallahu Alaihi Wasallama)).

Pɑge 1 & 2

“Usainah Usainah, tashi ki shirya mana mu fita da wuri, kin san fa idan muka makara shi kenan ba za mu samu aikin nan ba ko. Don Allah ki tashi, kin ga shekaranjiya ma ba mu samu shiga ba sakamakon ba mu je da wuri ba.”

Dakyar wacce ake tashi daga barcin wato Usaina, ta mike idanuwanta a tamaimaye da barci tamkar ma a lokacin ta kwanta, sannan ga wata azababbiyar gajiya da ta game mata duk gaɓɓan jikinta. Hatta da ‘yan tsunta dakyar take motsa su.

Haka ta lallaɓa ta mike ta fito ta nufi bayin gidan, inda ta iske mutane uku na jiran na ciki ya fito sannan su shiga. Ita ma sai ta hau layi ta zama ta huɗu kenan, kusan mintuna ashirin tana jira sannan layi ya zo kanta, ta shiga ta kamo ruwa ta fito ta yi alwala ta yi sallah lokacin har rana ta fara fitowa sosai kamar misalin karfe 7:00am na safe.

Tana idar da sallar Hassana ta ce, “To tashi mu tafi, kin ga har rana ta fara yi, shi yasa nake tashin ki tun da Asuba ki shirya kafin kowa ya tashi a fara wannan layin shiga bayin na ƙaddara.” Nan suka mike suka yi wa Inna, mahaifiyarsu sallama suka fice.

Hanya suka mika santal suna ta sauri kamar za su tashi sama, har da sassarfa suke haɗawa, sun yi tafiya kamar mintuna goma sha biyar (15 minutes) sannan suka isa wani kamfanin aikin barkono dake rukunin kamafanoni na unguwar Dakata.

Cikin sa’a suna shiga aka rufe kofar, su ne na ƙarshe da za su samu damar yin wannan aiki a wannan rana. Ba tare da ɓata lokaci ba ƙaramin manajan ya rubuta sunayensu a wani littafi da ake ɗaukar sunayen wanda suka samu basirar yin aikin, suka shiga cikin store din suka kama aiki.

            ******

Wadannan yara, Hassana da Usaina kamar yadda kuka ji sunansu, ‘yammata ne ‘yan kimanin shekaru  sha bakwai zuwa sha takwas (17-18) da haihuwa. Zaune suke a unguwar Tudun Wada tare da iyayensu wanda suka kasance masu ƙaramin karfi ainin.

Rayuwarsu cike take da ƙunci da talauci da rashin tabbas me tsanani. Ɗaki ɗaya ne tak! Suke rike da shi a gidan da suke haya, kuma su biyar ke kwana a cikin wannan daki wanda shi ma ba wani babba ɗaki ba ne. Hassana da Usaina da Inna da babansu, sai ɗan ƙaramin kanensu ana kiran sa Khalid, duk da kasancewar su Hassana baligai ne haka suke gwamutsuwa da mahaifinsu a wannan daki komai tsananin zafin da ake yi kuwa.

Mahaifin nasu ana kiransa malam Isah, ya manyanta sosai sannan ya gamu da larurar cutar laka (Spinal Cord). Kafin ya gamu da cutar ya kasance me sana’ar wanki da guga ne. Mahaifiyarsu kuwa sunanta Saude amma Inna suke ce mata.

Ba iya kamfanin barkono kadai suke zuwa aikin ba,  dukkan wani kamafani da ake daukar leburorin wucin-gadi, su Hassana zuwa suke su yi aiki. Ya danganta da lokaci da kuma nau’in abin da ake sarrafawa a kamfanin. Sukan yi aiki a kamafanin Ƙaro, kamfanin Riɗi kamfanin Citta da dai sauransu.

Wannan aiki da su suke yi shi ne cinsu, shi ne shansu, shi ne suturar da suke sawa, shi ne kudin maganin cuta karama idan ta same su, uwa uba shi ne kuma hanyar da suke samun kudin biyan hayar dakin da suke zaune a ciki. A takaice dai Hassana da Usaina sune ke rike da iyayen nasu da kuma ƙanensu Khalid.

A yini ɗaya ba sa yin aikin da ya wuce naira ɗari biyar (N500) kowacce daga cikinsu komai kokarin da za su yi. Su ne ma masu kokarin, domin wasu ba sa wuce su yi aikin dari uku ko dari hudu ba.

A cikin dari biyar din nan za su ci abincin rana bashi kafin su gama aikin a biya su, abincin safe kuwa ba samu suke ba, sai kamar ranar da Allah Ya sa suka yi tuwo da daddare ya yi saura, to da safen sukan samu su ci koda babu ɗumame.

Idan suka fita tun safen nan suka kama aiki ba sa tsayawa sai misalin karfe ɗaya zuwa biyu 1-2 na rana, a lokacin ne za su samu wani abin su ci, kamar dambu, alala, ɗanwake da dai dangain abincin garau-garau da masu sayarwa ke kaiwa kamafanin. Bayan sun ci wannan abinci, wasu kan yi sallah wasu kam babu ruwansu da sallar ma.

Bayan nan za su koma su sake kama aikin sai kuma yammaci sosai misalin karfe 5:00pm sannan za su dakata. Manajan zai zo da littafin nan da aka dauki sunayensu, za su kafa layi ana kiran sunayen nasu ɗaya bayan ɗaya ana ba su kudin aikin da suka yi.

Gwargwadon kokarin mutum gwargwadon abin da zai samu, Hassana da Usaina kan dage sosai su mayar da hankali akan aiki, domin indai har sun samu damar yin aikin, to ladansu ɗari biyar – biyar ne; idan aka haɗa jumulla sun kama naira dubu ɗaya daidai (N1,000).

Da zarar sun karɓi wannan kudi sai masu abincin nan su ma su taso domin su karɓi hakkinsu. Da yake Hassana da Usaina ba wani zagewa suke su ci abincin ba sosai, bai fi su kashe naira ɗari da hamsin ba (N150), dan haka sukan koma gida da aƙalla naira ɗari takwas (N800).

Ba su dawo gida ba sai daf da magariba, to dayake sun san yadda suka bar gidan nasu babu wani abin taɓawa. Naira ɗari da hamsin ce kacal a hannun Inna, da safen Khalid ya sayo musu koko da ƙosai na naira saba’in, da rana kuma ya sayowa baban nasu kunun tsamiya ya ɗan kurɓa. Saboda haka tun daga kan hanya Hassana da Usaina suka auno garin kwaki suka yo cefanen miya.

Isowarsu gida keda wuya Usaina ta haɗa wuta ta yi musu teba suka ci. Bayan sun gama cin abincin sun yi sallar Isha, jim kaɗan Hassana ta ce, “Usaina shirya mu tafi Islamiyya, kin san yau laraba akwai haddar Ƙurani kuma da wuri malam Musa yake shigowa.”

Usaina ta mike ta zira hijabinta suka dauki jaka suka fice. Misalin karfe 9:30pm suka dawo, nan suka ci gaba da hira da Innar tasu har kusan karfe 10:00pm na dare. Innar ta ce, “Ku tashi ku je ku kwanta ku huta domin ku tashi da wuri gobe.”

Wannan ita ce irin rayuwar da waɗannan ‘yammata suke yi tare da mahaifansu. Mahaifinsu ba mutumin Nigeria ba ne, daga Nijar ya zo, sannan ba wasu ‘yan uwa ba ne dabshi sosai, domin ita kanta Inna bai fi sau biyu ba ne ta taɓa zuwa Nijar ɗin. Su Hassana kam ba su taɓa sanin cewa Mahaifin nasu mutumin Nijar ne ba.

Farkon da larurar ta same shi, an kai shi asibiti an nemi kudin da za a masa aiki kusan naira milliyan ɗaya, kuma sai an aje wannan kudi, za a taɓa shi. Wannan al’amarin ba ƙaramin tada hankalin Inna da su Hassana ba ya yi, shin ina za su samu waɗannan kuɗaɗe haka da ba su taɓa ganinsu ba balle su san ma yawansu?

Da farko dai Inna wajen wani wanta ta je ta kai masa kukanta. Shi dai wannan wan nata ya kasance me hali ne sosai. A kasuwar kofar ruwa yake ɓangaren ‘yan rodi, babu shakka yana da kuɗi. To sai dai ya kasance irin mutanen nan ne mararsa adalci, marasa imani masu wulaƙanta zumunci, ba shi da kirki ko kaɗan mutumin banza ne.

Bayan sun gaisa ta gabatar masa da ƙoƙon bararta da ya taimaka mata koda ma bai biya kudin duka ba, ya dan ba da kafin alƙalami idan ya so ita ta shiga rigar arziki wajen masu hannu da shuni na unguwar tasu ta barato sauran. Mutumin nan sai ya ƙeƙasa-ƙasa ya murtuke fuska ya haɗa girar sama da ta ƙasa, ya haɗe rai kamar wanda aka aika wa da labarin mutuwa ya ce, “Yanzu fa kasuwa babu ciniki, zama kawai ake yi idan an je, babu harka saboda haka ayi hakuri sai dai nan gaba. ”

Inna ta fara masa magiya don Allah ya taimaka koda rabin kudin ne ya ba su a samu a ceto rayuwar bawan Allahn nan.

Matarsa ma ta sa baki da cewa, “Alhaji don Allah ka duba wannan buƙata ka ceci lafiyar mutumin nan, ka duba zumunci.”

Tsawa ya daka mata tare da cewa, “Ke dakata mini don Allah, ku me yasa mata yawancinku ba ku da tunani ne ko kaɗan? Ta ya ya kasuwa ba a samun ciniki kawai sai a ɗebi kudi aje wani waje can daban inda ba a da tabbas ɗin za a amfane su. Karki sake mini irin wannan, idan ina magana da mutane kada ki ƙara saka mini baki.”

Ta ce,“Allah ya huci zuciyarka ka yi hakuri ba zan sake ba.”

Nan dai Inna ta taso gwiwarta a doke tamkar an sa sanda an doke mata su, ta yi dana sani da nadamar zuwa wajensa.

Ku taba link din nan dake ƙasa domin shiga group dinmu a BAKANDAMIYA

https://bakandamiya.com/group/95/pen-writers-association
                   

*αввαи αιѕнα*   

                   *•••мαтαkıη ηαsαяα 2020*

KUDA BA KA HARAM 49-50

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝 *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 🐝🐝🐝🐝🐝🐝 🐝🐝🐝🐝 🐝🐝🐝 🐝🐝 🐝

❝Imɑm Shɑfi’i yɑ ce: “Zinɑ bɑshi ce, ‘yɑ’yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ ‘yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ ‘yɑrkɑ kyɑutɑ.❞
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫

Written by:
Sɑdik Abubukɑr

Wɑttpɑd @sɑdikgg

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

Shɑfi nɑ 49 & 50

BAYAN SATI DAYA

To kawo yanzu dai bamgaren makarantar su Humaira, sun kusa kammala ajin farko wato level 100, bai fi saura mako biyu ba su fara rubuta jarabawar second semester (wato, zango na biyu). To a iya cewa ba ta sauga zane ba a bamgaren Humaira, domin tana nan dai babu yabo babu fallasa ko a ce ma gara jiya da yau. Ita dai da ma ta kasance irin mutanen nan ne masu karancin fahimta karatu, ana matukar shan wahala kafin su fahimci inda malami ya dosa. Sannan kuma ga rashin mayar hankali da ba ta yi, ta saka shashanci da sakarci a rayuwarta. Zuwa makarantar kawai take amma sam kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.

Ita kuwa Binta abinta sai san-barka, domin arziki ne ya ci uban na da, ma’ana ta ribanya kwazonta sosai. Duk da cewa ta samu maki mafi yawa a tsangayar tasu hakan bai sa ta yi wasa ko kuma ta ce ai ita ta samu tudun dafawa ba, a madadin haka sai ta sake bude wuta, ko ba komai ta ci gaba da rike kambunta na gwarzuwar daliba mafi kwazo a ajin nasu.

Haka nan kuma ba ta gajiya ba wajen ba wa kawar tata shawarwarin da fahintar da ita abin da ba ta gane ba. To sai dai ita Humaira ba ta bukatar hakan sam, ta fi ganewa zama cikin su Ruky suna haduwa suna shashanci tare. Kowa dai ya san wace Ruky da kawayenta, ba karatu baya ne a gabansu, ba sa bibiyar darusa, su dai ‘yan follow up ne. Aikinsu shi ne bibiyar malamai masu budurwar zuciya da halin dan akuya domin samun maki, koda irin jeka da hanlinka din nan ne. Wato dai suna yin tsarin nan ba ni gishiri na ba ka manda. Ba irin kokarin da Binta ba ta yi ba akan ta ganar da Humaira illar rashin mayar da hankalinta akan karatu amma sam ba ta ji, ta sa auduga ta toshe kunnenta. Wanda ya yi ya nisa ba ya jin kira.

Duk da cewa Binta na zuwa café din Sadik tana taya shi aiki, hakan bai hana ta ware wani lokaci ba don yin bitar karatun da aka yi musu tare da Humairar, amma sai ta ki bayar da hadin kai.

Bayan cikar wa’adin makonni biyu suka fara jarabawa kamar yadda aka tsara, shirin zaune ya fi na tsaye, in ji masu iya magana. Binta ta shirya wa jarabai sosai fiye da shirin da ta yi a baya, ta yi karatu matuka har sai da ta ji ba dadi. Don haka duk jarabawar da ta shiga cikin fara’a da murmushi take fitowa daga hall din. Sabanin gogar taku, ita kam babu abin da ya dame ta. Takan fito ne fuskarta kadaran kadahan, kwatankwacin yadda ta yi jarabawar zangon farko haka wannan din ma ta kasance.

Suna kammala jarabawar hutun makonni biyu ne aka ba su kuma a cikinsa ne ake son su yi registration na aji biyu, wato level 200. Ranar da suka gama jarabawar kafin su bar makarantar, Sadik ya ce da Binta yana son ganin ta kafin ta tafi gida akwai maganar da za su yi. Gabanta ya yanke ya fadi, nan take ta fara sake-sake, “To wace magana za mu yi da shi ne? Allah Ya sa dai abin da nake tunani ne, sai dai kuma fa yanzu ina matukar jin Anty Meenat. Na lura da take-taken yaya Sadik so yake ya jirge burinsa na Humaira akaina, anya kuwa abin nan zai yiyu?”

Tunanin da Binta ta yi ke nan jim kadan bayan Sadik din ya sanar da ita. Wani nishi ta ja sannan kuma ta sake nutsawa cikin wani tunanin kamar haka, “To amma kuma fa burina ke nan, ina son yaya Sadik sosai wallahi. Mutumin kirki ne matuka, koda ba na son sa muddin ya nuna mini bukatarsa to ba zan juya masa baya ba. Shi din dan halak ne ya cancanci a ba shi ajiyar zuciyar domin ya san kimarta kuma zai kula da ita yadda ya dace.”

Tana kaiwa karshen wannan tunani ta saki wani lafiyayye kuma lallausan murmushi tamkar a gaban Sadik din take, Humaira ce ta ce da ita, “Ke kuma kanki daya kuwa kike ta murmushi ke kadai, ko wani daddadan albishir aka yi miki ne?”

“Hmm! To ai shi murmushi ba sai an yi wa mutum albishir din komai ba zai yi shi. Yin murmushi sunna ce, kuma idan mutum ya tuna wani abin farinciki ma zai yi murmushi.”

A yatsine Humaira ta dubi Binta ta ce, “Allah ko? Yo ke wane abin farinciki za ki tuna da zai sa ki nishadi da murmushi da ya wuce karatu, kullum kina cikin kallon takarda. Ki bi dai a hankali wallahi kada ki samu matsalar ido da kuruciyarki, masu idon ma ya suka kare bare kin zama musaka.”

Ta karasa maganar da sakin wata matsiyaciyar dariya, murmushin Binta ta ci gaba da yi tana cewa, “Haka dai kika ce, amma Dan Adam a rasa abin da zai sa shi farinciki? Kuma wa kika taba jin cewa karatu ya makantar?”

Daidai lokacin da suke wannan tattaunawa karfe 1:00pm na rana ne, wato fitowarsu daga jarabawar karshe ke nan. Wasu daliban ma har sun fara tafiya gida, Humaira ta ce, “To na ji, bari na je wajen Ruky mu yi sallama kafin mu tafi ko?”

A yatsine Binta ta amsa mata da cewa, “Idan kin gama ki same ni a wajen Sadik.”

“Wace za ta zo wajen Sadik? Allah Ya tsari gatari da saran shuka, idan kin ga flashing kawai ki taho mu tafi kin ji amma ni ba zan zo ba.”

“To na ji.” Binta ta fada tare da kama hanyar café din. Ta tsani tarayyar Humaira da Ruky, da a ce tana da yadda za ta ta raba su da ta yi, kawancen ba na alkairi ba ne sam.

Tana isowa café din ta iske Sadik ne shi kadai, “Ina Anty Meenat din?” Ta tambaya.

“Yau ta tafi asibiti, watakila ma ba za ta zo ba daga can gida za ta wuce.”

“Ayya! Allah Sarki! Jikin ya fara nauyi ko? Allah Ya sauke ta lafiya.”

“Amin Ya Allah.” Ya fada fuskarsa cike da murmushi. Suka yi shiru na wasu ‘yan dakiku ba wanda ya yi magana, zuwa can ya katse shirun da cewa, “An kammala jarabawa ko? Sai hutu ke nan.”

Ta saki murmushi me dan sauti tare da cewa, “E amma ai ba hutu ba ne me yawa.”

“Haka ne, ba shi da waya kam. To yanzu za ki wuce gida ke nan?”

“Hmm! A’a zan tsaya mana tunda na ga akwai aiki kuma Anty Meenat ba ta nan, aikin yawa zai yi maka.”

Cikin yalwataccen murmushi ya ce, “No, kada ki damu da wannan aikin, ba karewa yake ba, sai dai mu yi abin da muka yi. Idan babu damuwa ina son mu je gida na gai da magabatanki.”

Farinciki hade da tsoro ne suka ziyarci zuciyarta lokaci guda, abin da take buri yana neman faruwa, a hannu guda kuma ta fara tunani da wace fuska za ta kalli Meenat idan abin ya tabbata? Gaskiya akwai cakwakiya a wannan lamari, Allah Ya shiga lamarin idan hadin na Ubangiji ne ba makawa sai abin ya tabbata, to sai ya kimsa wa zuciyarta dangana da fahimta. Tunanin da Binta ta yi ke nan wanda ya tsawaita mata yin shiru ba ta ba wa Sadik amsa ba, katse mata tunanin ya yi da cewa, “Ya ya dai kika yi shiru? Ko akwai matsala ne?”

“Hmm! Babu wata matsala, kawai ina tunani ne Humaira ba za ta yarda mu tafi tare ba. Ba za ta shiga motarka ba, kuma ka ga tare muke tafiya. Idan na ce ta tafi ba za ta ji dadi ba, sai ta ga kamar na yi mata wulakanci ne. Kawai zan yi maka Kwatancen layinmu, idan ka zo sai ka yi mini waya, ko ya ka gani?”

“Good! Haka ne, kin yi tunani me kyau. To ban sani ba ko akwai wani abin da za ki rika yi a gidan kafin ku dawo karatu, da ina son ki ki rika zuwa koda kwanaki uku ne ,saboda kin ga Meenat jikinta ya yi nauyi na san dole ta rika hutawa.”

“To shi kenan zan fada a gida In Sha Allah za a amince.”

“Yawwa!” Ya fada tare da bude wata drawer kusa da shi ya dauko Scratch Card na makarantar wanda idan dalibi ya biya kudin registration a banki za a ba shi, da Scratch Card din ake amfani wajen yin online registration. Mika mata ya yi tare da cewa, “Ga wannan ki ajiye shi idan an bude muku portal sai ki yi registration na level 200.”

Cike da murna da farinciki take duban sa, musayar murmushi kawai suke wa juna, ta gaza magana. Ya sake bude wata drawer ya dauko kudi naira dubu ashirin cif ( ₦20000), ya mika mata yana cewa, “Wannan kuma kudin aikinki ne na wata daya, karbi mana.”

Sunkuyar da kanta ta yi ta ki karba, ya ci gaba da magana, “Cewa ki karba, kudinki ne.”

Mursisi ta ki koda dago kai, a sunkuye ta ce, “Yaya Sadik don Allah ka bari, ni wane aiki na yi da har za a ba ni kudi? Wannan Scratch Card din ma da na san za ka sayo shi wallahi da ba zan zo ba.”

“Ban gane ba za ki zo ba, shin akwai abin da kika tambaye ni ne a ciki? Registration da na yi miki kyauta ce tawa, sai dai idan kuma ladan ne kike mini rowar samu. Wannan kudi kuma na fada miki hakkinki ne dole ne ki karba.”

“To shi kenan na gode sosai Allah Ya kara girma da daukaka, Allah Ya saka da mafificin alkairi. Amma ka bar kudin na gode, bari na je na samu Humaira tana jira na kada ta yi fushi.”

Ya dan sauya fuska alamun fushi sannan ya ce, “Hmm! Kamar ba kya fahimtar abin da nake cewa, su wadannan kudade ba kyauta ba ce na yi miki, guminki ne wanda Allah Ya yi umarni da a ba ki. Kin yi mini aiki a nan tsawon wata guda, don haka wajibi ne na biya ki kudinki. Ko Meenat ma da kike gani haka nake ba ta kudinta duk wata, yanzu haka ga nata zan ba ta idan na koma gida. Ina fatan yanzu dai kin fahimta?”

Ta yi murmushi me dan sauti sannan ta ce, “E na gane duk abin ya kake nufi, amma ni na yafe nawa hakkin ka bar shi.”

“Hmm! To ko dai kin rena ne?”

Ta yi saurin dago kai hade da sakin wata siririyar dariya sannan ta ce, “Lah Yaya Sadik! Wace renuwa kuma zan yi, to ni wane aiki ma na yi har da zan rena kudin da za a ba ni? Ni dai kawai na ce ka bar shi ne ban yi don kudi ba.”

Ganin yadda ta kafe, ya buga ya raya ta karba ta ki sai ya kyale ta. Duban ta ya yi ya ce, “To shi kenan tunda kin ki karba, yanzu sai ki yi mini kwatancen unguwar taku.”

“Hmm! Yawwa, idan ka zo Jakara daidai ofishin ‘Yan Sanda sai ka yi mini waya.”

“Okay, In Sha Allah za ki ji ni bayan La’asar.”

Rufe bakinsa keda wuya sai wayarta ta fara ruri, Humaira ce ta kira ta, tana dagawa kafin ta yi magana Humairar ta magana da masifa, “Ke malama idan kin gama ina jiran ki, ki zo mu wuce. Idan kuma ba zai bar ki ba ki tafi to ki sanar da ni.”

Dayake wayar Binta na da kara sosai, Sadik ya ji duk abin da Humaira ta ce. Binta ta dan bata rai kadan sannan ta ce, “Ke wai me ya sa kike haka ne? Komai abin masifa ne, ke din ba uzurinki kika tafi ba wajen su Ruky.”

“Okay, lallai ba shakka, dole ki hayayyako mini ya fara zuga ki ko?”

“Kin ga ni ya isa haka gani nan kawai.”
Binta ta fada tare da kashe wayar ta juya ga Sadik, murmushi kawai yake saki. Muryarta a sanyaye ta ce, “Yaya Sadik don Allah ka yi…”

Ya yi saurin katse ta da cewa, “Ba komai kada ki damu, ni ai ba sai kin fada mini wace Humaira ba? Ko kin manta ne? Ki je ku ta fi kawai sai kin ji ni anjima din.”

Jakarta ta dauka ta mike ta fito, shi ma fitowar ya yi, ya biyo bayanta da naira dubu biyu a hannu ya ce, “To karbi kudin mota ko?”

Ba ta son su sake ja’inja da shi, don haka sai ta zari dubu daya ta bar masa dubu daya, tana sakin murmushi ta wuce. Tana isowa wajen Humaira, wata hararar renin wayo Humairar ta jefe ta da ita, dayake Binta ba ta son su rika sa’insa sai ta yi kamar ba ta gani ba ,ta saki fuska cikin sigar wasa ta ce, “Ke dadina da ke saurin fushi, don Allah ki rika shan ragowar ruwan alwala ko kin rage saurin hawan nan.”

“Haka ma za ki ce ko? Na ga alama Sadik so yake ya raba mu, kin fi jin maganarsa sama da ta kowa. Duk abin da ya ce miki shi kike yi, ki kula dai wallahi matarsa ‘yar Katsina ce, asiri ne da su kamar me. Idan kina son rasa mijin aure kwata-kwata har abada, to ki ci gaba da yin soyayya da mijin ‘yar Katsina.”

Dariya ta yi sosai har sai da Humaira ta fara jin haushi sannan ta ce, “Wallahi na dade ban ji abin dariya ba kamar wannan maganar taki, gaskiya za ki yi kyau da fitowa a irin shirin nan na comedy. Yanzu wato ke tsoron asirin Katsinawa ne ya sa tun farko ba ki karbi soyayyar yaya Sadik din ba lokacin da ya nuna yana son ki?”

Tana fada ta sake tintsirewa da dariya, a wannan karon har da dafa kafadar Humairar sannan ta ci gaba da cewa, “To tunda ke tsoron asiri ya sa kin rabu da kyakkyawan namiji, daya tamkar da dubu. Mutum me cikar kamala da kwarjini wanda ya san kima da darajar ‘ya mace, to ki saurara ki ga yadda zan yi soyayya da shi kuma na mallake shi a hannuna a matsayin mijina. Ba ‘yar Katsinawa ba ko ‘yar bokayen Indiya ce ba ta isa ta hana Allah ikonSa, da yardar Allah sai na auri yaya Sadik. Allah ba zai jarabce ce shi da son mu ba, mu biyu kuma kowacce ta watsa masa kasa a ido ba. Ke dai tunda ba kya yi, to ni zan share masa hawaye, zan shayar da shi zumar soyayyar da yake muradi matukar ina numfashi a doron kasa.”

────────────────────────────
Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ. *_•••©ᴀʙʙᴀɴ ᴀɪsʜᴀ_*

💝💝💝SAHURA0⃣7⃣💝💝💝

💖💖💖 *_SAHURA_* 💖💖💖

Written by:
         Sadik Abubakar

Wattpad @sadikgg

*_Wannan labari kirkirarre ne, banyi dan muzanta rayuwa wani ba. Idan ya dace rayuwar ka, akasi aka samu._*✏️✏️✏️

*Page 0⃣7⃣*

*_(Na sadaukar wannan ga malama ta primary Malama Murja Ali Ado Asibiti, Allah ya jikanki Allah ya jaddada rahama gareki 😥 amin summa amin.)_*

Kama hannun sa tayi ta girgiza sannan ya yi juyi hade da mika, “Kai da Allah ka tashi haka gari ya waye tuntuni, ka tashi kayi sallah kazo kayi breakfast.” Nan ya yunkura idanun sa dakyar suke budewa.

Juyowar da Umma zata yi kafar idon ta a kan kwalbar syrup din nan, “Inna lillahi Wa Inna ilaihir raji’un!’ Ta fada dai dai lokacin da ta dafe kirjin ta fuskarta ta sauya lokaci guda sannan ta cigaba da cewa, “Salim abinda ake fada min a kanka ashe gaskiya ne?. Yanzu rayuwar da zaka jefa kanka kenan, shan miyagun kwayoyi, me ya hada ka da wannan maganin?”

“Haba Umma dan Allah, me yasa kike fadar haka, wai me nake yi ne, wallahi kawai yaya Faruk ne ya samin ido, yau ne fa kawai na sha  wannan maganin saboda na gaji ina son inyi bacci sosai.”

Umma tace, “Gajiyar uban me kayi, aikin me kake yi da zaka gaji? Me ka nema a gidan nan ka rasa? To ka saurareni sosai, wallahi a wannan zuwan da Abban ku ya yi bayan Faruk ya fada masa duk rashin mutumcin da kake, cewa ya yi zai kaika a sa maka mari, ni ce na bashi hakuri. Amma wallahi muddin ka sake komawa wannan shaye-shayen zan cire hannu na daga maganar ka, zan kyale shi ya yi maka duk irin hukuncin da ya gadama, babu ruwa na da kai.”

“Umma kiyi hakuri shike nan na daina, ba zan sake ba.”

Umma tace, “To shike nan ka tashi kaje kayi sallah kazo kayi breakfast ga abincin ka can a kan table.”

Bayan kwanaki biyu kenan da kaiwa Baba Abu korafin Umma, sai ta shirya tun da safe tayowa gidan tsinke domin ta zo taji ba’asin da yasa Umman take abubuwan da basu kamata ba. Misalin karfe goma na safe 10:00am ta iso gidan. Kai tsaye ta shiga tayi sallama, Sahura ce a tsakar gidan tana wanke-wanke, ta ajiye da sauri ta mike cikin fara’a da murna ta tarbi Baba Abu, “Sannu da zuwa Baba.”

Baba Abu da fara’arta ita ma ta amsawa Sahura, “Yauwa Sahura sannu da kokari, ina mutanen gidan?”

Sahura tace, “Suna falo ki karasa.” Kafin ta gama rufe bakin ta tuni Hafsat ta jiyo muryar Baba Abun, a guje ta fito daga falon tazo ta rungume Baba Abu tana fadin, “Oyoyo oyoyo” ta jata sukai falo. Umma ce zaune a kan kujera, mikewa tsaye tayi ta tarbi Baba.

Wani mamaki da tunani Umma ta tafi na dan wani kankanen lokaci dangane da zuwan mahaifiyar ta ta a irin wannan lokacin haka. Anya lafiya kuwa? To me ke faruwa kuma Baba da safe haka, bama zata aiko haifa ba da kan ta?

Wannan tunani da kuma yadda Baba Abun ta sauya fuska dai dai lokacin da suka hada ido, yasa ta dan sha jinin jikin ta, amma sai ta kanne kawai tace, “Sannu da zuwa, da safe haka kike tafe, ince ko dai lafiya?”

Baba Abu bata bawa Umma amsa ba, sai ta zauna bisa kujera, ita ma Umman kan kujerar ta koma ta zauna tare da umartar Hafsat da ta kawowa Baba ruwa da lemo, ta kuma zubo mata abinci. Nan take Hafsat ta make ta nufi kitchen. Kafin Hafsat ta dawo, Umma ta zame daga kan kujera tare da risinawa, ta gaida Baba cikin ladabi da girmamawa, “Ina kwana ina gajiya, ya kuke ya gidan.”

Baba Abu wacce ta dan hade rai ta amsa mata, “lafiya lau.” Umma ta cigaba da cewa, “Ya ya sahu kuma, kina fama da kafa, ai da kin aiko Halifa ma, ince dai lafiya koh? “Baba Abu tace, “Ai sakon yafi karfin aike.”

Komowar Hafsat daga kitchen ta katsewa Baba Abu martanin da ta fara mayarwa. Farantai biyu ne ciccike, daya na abinci daya kuma kayan ruwa da lemuka ne, ta aje gaban Baba Abu tace, “Yar tsohuwa ga abinci nan kici ki koshi kinji nasan kin yi tafiya ki huta.” Wata harara Umma ta aika mata wacce ta katse mata tsokanar da take wa kakar ta ta, sai ta mike ta nufi dakin su.

Falon yayi shiru na wasu ‘yan dakiku kafin daga bisani Baba Abu tace, “Saratu me yasa har kullum ke ba zaki girma bane. Ace har kawo yanzu baki san Annabi ya faku ba, ba zaki iya magance matsala ba idan ta taso miki, ko kuma ince ma ke ce da kanki kike kirkirowa kanki matsalar.”

“Baba to me kuma aka ce nayi yanzu, wani abin ne ya faru kuma, wallahi mutane dai basa kyautawa, gulma da munafurci sunyi yawa, wani ne yace miki nayi wani abun?”

Baba Abu ranta a bace tace, “Saratu ina guje miki fishin Ubangiji, billahillazi idan baki sauya halinki da mu’amalar ki ba a kan yaran nan,  zaki hallaka kanki. Faruk ne ya kai min korafin kin daina masa magana kuma idan ya gaishe ki bakya amsawa a kan ya nusar dake wani kuskure da kike aikatawa bisa amanar marainiyar yarinyar nan.

Shin yanzu ba abin kiyi farin ciki bane tare da godewa Allah, da ya baki yaro nutsatstse wanda zai ga kinyi abinda bai dace ba ya nusar dake? Amma saboda sakarci sai ki dorawa yaro karan tsana? To ina so ki saurareni sosai da kunnen basira, kar inji, kar in sake gani.

Yaron nan yana da kyakyawan hali, ki hada kai dashi, hatta Salim dake rashin jin nan da kin bawa Farukun dama da goyon baya da ya ladaftar dashi, dan uban shi tunda ba shi ya haifi kan sa ba. Sannan kuma dangane da ita Sahura, daga yau din nan, ke daga yanzu ma ina son ki dauke ta tamkar ke kika tsugunna kika haife ta.

Duk abinda zaki so ya samu Hafsatu, to ki sowa Sahura shi fiye da Hafsatun, haka zalika duk wani abu da kike gudun ya samu Hafsatu, to ki karewa Sahura shi da dukkan karfin ki da iyawar ki. Bana son na sake jin wani abun cutarwa ya sake taba wannan yarinya, ki hada kansu gaba daya, Allah ya shiryar miki dasu, Allah ya yi miki albarka.”

Umma, wacce kanta ya ke kasa tun lokacin da Baba ta fara fada, sai yanzu ta dago kai tare da sakin ajiyar zuciya sannan tace, “Shike nan Baba naji kuma insha Allahu zan kiyaye, kici abincin kada ya yi sanyi. Kiyi hakuri hakan ba zata sake faruwa ba, nagode.”

Baba Abu ta dan yaiyatsini abincin sama-sama, tasha ruwa. Suka dan taba wata hirar daban. Sai misalin karfe sha-biyu 12:00pm na rana sannan tayi shirin komawa. Umma tayo mata rakiya har bakin titi, ta tare mata dan sahu drop, ta biya shi har gida ya kawo ta…..

*_Gareku readers, babu abinda marubuta suke bukata especially online writers, face comments, like, vote and share_*

Domin gyara, shawara ko sharhi aiko ta email:- insado26@gmail.com

*Ku dakace ni,*

*Whatsapp: 08163478965

*wattpad: follow @sadikgg

Design a site like this with WordPress.com
Get started